"Dole na Yi Bayani," Ministan Tinubu Ya Tunkari Atiku kan Batun Bude Iyakokin Najeriya
- Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce iyakokin Najeriya ba a rufe suke ba, don haka babu abin da za a sake budewa
- Tunji Ojo ya bayyana cewa tsaurara matakan tsaro a wasu iyakokin Arewa ya samo asali ne daga barazanar ‘yan bindiga da sauran ‘yan tada kayar baya
- Ya kalubalanci Atiku Abubakar da ya gabatar da cikakkiyar manufa kan kula da iyakokin kasar maimakon hada batutuwan kasuwanci da tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Harkokin Cikin Gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo, ya yi watsi da ikirarin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, cewa har yanzu iyakokin Najeriya a rufe suke.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja, ministan ya mayar da martani kan kalaman Atiku na cewa zai sake bude iyakokin kasa na Najeriya idan aka zabe shi a 2027.

Kara karanta wannan
"Me ka ke nufi?" Fadar shugaban ƙasa ta maida martani ga Atiku kan buɗe iyakokin Najeriya

Source: Facebook
Minista ya maida martani ga Atiku
Vanguard ta ce Tunji-Ojo, wanda ke kula da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS), wacce ke da alhakin kula da iyakoki da harkokin shige da fice, ya ce ya zama dole a gyara wannan fahimtar.
“Ni a matsayina na Ministan Harkokin Cikin Gida, wanda ke kula da Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, wacce ita ce hukumar gwamnati mai kula da iyakoki, ya zama dole a bayyana cewa iyakokin Najeriya ba a rufe suke ba, don haka ba za a sake bude su ba,” in ji shi.
Ya bayyana yadda aka rika bude wasu daga cikin iyakokin kasar a cikin shekarun baya, inda ya ce gwamnatin da ta gabata ta sake bude iyakokin Seme, Illela, Maigatari da Mfum a ranar 16 ga Disamba 2020, sannan aka bude wasu daga baya.
Yadda aka sake bude iyakokin Najeriya
Ya ce an sake bude Idiroko da Ikom domin zirga-zirgar da ayyuka a ranar 20 ga Afrilu 2022, yayin da aka sake bude Kamba da Tsamiya a Jihar Kebbi, wadanda ke hada Najeriya da Jamhuriyar Nijar da ta Benin, a watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan
Babbar magana: An yi kaca kaca da shirin Atiku na bude iyakoki da dawo da tallafin fetur
Tunji-Ojo ya soki kalaman Atiku kan Kamaru, Chadi, Nijar da Benin, yana mai cewa dogon lokacin da aka shafe ba a bude iyakar Kamaru da ke Banki da Amchidé ba shi da alaka da manufar kasuwanci ta shekarar 2019.
“Rufe iyakokin Najeriya da Kamaru da ke Banki da Amchidé na tsawon lokaci bai samo asali daga manufar kasuwanci ta 2019 ba.
"Sun rufe ne tun 2014, lokacin da Boko Haram ta tilasta rufe su saboda dalilan tsaro, sannan aka sake bude su a 2019, yayin da aka bude Fotokol da Gambaru a 2021 bayan hadin gwiwar sojojin Najeriya, Kamaru, Nijar da Chadi wajen tabbatar da tsaro da daidaita yankin,” in ji shi.

Source: Facebook
Ministan ya ce hada wannan tarihi na matsalar tsaro da rufe iyakoki da aka danganta da harkokin kasuwanci na 2019 a matsayin abu guda ya gurbata fahimtar al’amuran biyu.
Tunji-Ojo ya bukaci kada siyasar neman mulki ta zama hanyar sauya tarihin baya-bayan nan, yana mai kalubalantar Atiku da ya gabatar da sabuwar manufa kan yadda za a inganta kula da iyakokin kasar.
Fadar shugaban kasa ta yi martani
Kun ji cewa Fadar Shugaban Kasa ta tanka wa Atiku Abubakar bayan ya yi alkawarin bude iyakokin Najeriya idan ya ci zaben 2027.
Hadimin shugaban kasa, Sunday Dare yce mafi yawan iyakokin Najeriya na kasa a bude suke tun daga watan Maris 2024.
Asali: Legit.ng