An yi wa Kwankwaso Wankin Babban Bargo da Ya Nemi Atiku Ya Janye Takarar 2027
- Jigon jam’iyyar ADC, Chille Igbawua, ya yi watsi da kiraye-kirayen tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2027
- Igbawua ya ce shekaru da kuma lafiyar Atiku ba hujja ba ce da za ta hana shi yin shugabanci, yana mai cewa har yanzu yana da ƙwazo da basirar jagoranci
- Jigon ADC ya kuma soki masu cewa ya kamata Atiku ya janye domin a kula da shi idan an samu nasara, tare da bayyana cewa hakan na ƙara raba kan jam’iyyun adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Jigon jam’iyyar ADC, Chille Igbawua, ya mayar da martani kan kiraye-kirayen tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2027.
Igbawua, wanda tsohon ɗan Majalisar Wakilai ne kuma mai ba shugaban ADC shawara, ya yi wannan bayani ne yayin wata hira.

Source: Facebook
A bidiyon da tashar Arise ta wallafa a X, ya ce ba a da wata hujja da ke nuna cewa shekarun Atiku ko lafiyarsa sun hana shi iya jagorantar Najeriya.
Magana kan shekarun Atiku
Igbawua ya ce shekarun da aka rubuta a takardar haihuwa ba su ne kawai abin dubawa wajen tantance ikon mutum na shugabanci ba.
Vanguard ta rahoto ya ce:
“Ban san inda aka samo bayanan da ke nuna matsalar lafiyar Atiku ba. Atiku bai canja shekarunsa ba, amma batun ko saboda shekarunsa ba zai iya mulki ba wani abu ne daban.
“Na san mutanen da suke cewa sun fi Atiku ƙuruciya, amma ba su da kuzari, basirar tunani da hikimar da Atiku yake da su. Don haka ba shekarun da ke kan takarda ne kawai abin dubawa ba.
“Har ila yau, shekaru suna da alaƙa da yanayin lafiya, kuma ban ga wata matsala daga cikin waɗannan abubuwa da za ta zama nakasu ga Atiku Abubakar ba.”
Raddin da aka yi wa Kwankwaso
Igbawua ya bayyana kalaman cewa Atiku ya janye domin jam’iyyar adawa ta kula da shi idan ta yi nasara a matsayin abin kunya.
Ya ce:
“A ce Atiku ya janye domin idan sun yi nasara su kula da shi, ta yaya? Wannan cin mutunci ne. Kula da shi ta wace hanya? Za ku biya masa kuɗin asibiti ne? Ko ku riƙa samar masa da abinci a gidansa?
“Ina ganin wannan magana rashin ya kamata. Ta yi matukar muni”
Ga bidiyon da ya yi bayani:

Source: Facebook
Maganar matar Atiku kan 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa matar ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Alhaji Atiku Abubakar, Titi Abubakar, ta ce mijinta ba ya buƙatar kuɗin ‘yan Najeriya idan aka zaɓe shi a 2027.
Titi ta bayyana cewa Atiku na son yin amfani da damar shugabanci ne wajen mayar wa al’umma abin da ya samu, tana mai bayyana shi a matsayin mai taimakon jama’a kuma gogaggen ɗan siyasa.
Ta ce Atiku ba sabon shiga ba ne a harkar shugabanci, kuma ba zai buƙaci koyon aiki daga farko ba idan ya samu damar jagorantar Najeriya a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng

