'Ban da Atiku,' Dan Takara 1 da Ya Bugi Kirji kan Shi Kadai zai Iya Maido Tallafin Mai

'Ban da Atiku,' Dan Takara 1 da Ya Bugi Kirji kan Shi Kadai zai Iya Maido Tallafin Mai

  • Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya ce shi kadai ne zai iya dawo da tallafin man fetur idan ya samu nasara
  • Sowore ya caccaki Atiku Abubakar, yana mai cewa bai kamata 'yan Najeriya su yarda wasu 'yan siyasa su canza tarihi kan batun tallafin mai ba
  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta bayyana yadda aka kashe kudaden da aka ce an samu bayan cire tallafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya bayyana cewa shi kadai ne zai iya dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi shugaban kasa.

Sowore ya ce jam'iyyarsa ta AAC ta tsaya tsayin daka tun farko wajen adawa da cire tallafin man fetur, sabanin wasu 'yan siyasa da yake zargi da sauya matsayinsu saboda maslahar siyasa.

Kara karanta wannan

Yan takara 3 da suka sha alwashin dawo da tallafin fetur idan aka zabe su

Omoyele Sowore a wani waje
Dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Sowore ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya mayar da martani kan kalaman tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kan yadda ake tafiyar da kudaden da aka samu bayan cire tallafin mai.

Maganar da Sowore ya yi

Sowore ya ce bai kamata 'yan Najeriya su bari Atiku Abubakar da sauran 'yan siyasa su yaudare su ko kuma su yi ikirarin cewa su ne suka fara adawa da yadda gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta cire tallafin man fetur ba.

A cewarsa, jam'iyyar AAC ce kadai ta bayyana matsayinta karara cewa ba za ta cire tallafin man fetur ba idan ta samu damar mulkin Najeriya.

Ya ce matsayinsu a taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) da aka gudanar a Port Harcourt ya sanya gwamnatin Tinubu cikin damuwa kan batun tallafin.

Sowore ya ce:

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta sake gano lam'a a shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

"Kada ku bari Atiku Abubakar da kungiyar masu yi masa dariya su yaudare ku kan batun tallafin man fetur ko su yi kamar su ne suka haddasa firgicin da yanzu ya mamaye gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu."

Ya kara da cewa:

"AAC ce kadai ta bayyana matsayinta karara cewa ba za mu cire tallafin man fetur ba. A lokacin da muka dawo daga Port Harcourt, Atiku ya riga ya sauya matsayinsa yana kokarin bin sahunmu."

Me Atiku ya ce kan tallafin mai?

Tun da fari, Atiku Abubakar, wanda shi ma dan takarar shugaban kasa ne na jam'iyyar ADC, ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi wa 'yan Najeriya bayanin yadda aka kashe kudin da aka ce an samu bayan cire tallafin man fetur.

The Cable ta rahoto cewa Atiku ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta cire tallafin tare da bukatar 'yan Najeriya su jure wahalhalun da hakan ya jawo, bisa alkawarin cewa za a yi amfani da kudin wajen ayyukan ci gaba.

Atiku Abubakar da Rotimi Amaechi
Atiku Abubakar da abokin takararsa a ADC. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Maganar da gwamnoni suka yi

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnonin jihohi 36 sun yi watsi da zargin cewa gwamnatocin jihohi sun kasa yin bayani yadda ya kamata kan kudaden da suka samu bayan cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: Atiku na neman bahasi daga Tinubu kan kudaden cire tallafi

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), AbdulRahman AbdulRazaq, wanda gwamnan Bayelsa, Douye Diri, ya wakilta, ya ce ba gaskiya ba ne cewa jihohi sun kasa yin bayani kan yadda aka tafiyar da kudaden.

Gwamnonin sun kuma nuna goyon baya ga shirin samar da sufuri mai saukin kudi ta amfani da iskar gas ta CNG, wanda ake sa ran zai taimaka wajen rage kudin sufuri a fadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng