Gwamna Uba Sani Ya Fadi Matsayarsa kan Batun Juyawa Tinubu Baya a 2027
- Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu tsakanin kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na kuri'un jihar a zaben 2027
- Uba Sani ya ce ikirarin cewa Arewacin Najeriya na juya wa Tinubu baya ya samo asali ne daga siyasar kafafen sada zumunta, ba hakikanin abin da ke faruwa ba
- Ya kuma ce jam'iyyar APC na da karfin gwiwar samun nasara a Kaduna da sauran yankunan Arewa sakamakon sauyin tsarin siyasa da ayyukan gwamnati.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa babu wani yunkuri na Arewacin Najeriya na juya wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya kafin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Ya ce hasashen cewa mutanen Arewa na adawa da shugaban kasa ya fi fitowa daga tattaunawar siyasa da ake yi a kafafen sada zumunta, ba tare da yin la'akari da hakikanin abin da ke faruwa a tsakanin jama'a ba.

Source: Twitter
Uba Sani ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television, inda ya yi hasashen cewa Tinubu zai samu tsakanin kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na kuri'un jihar Kaduna.
Batun nasarar Tinubu a Kaduna
Gwamnan ya ce Shugaba Tinubu, wanda ya samu kusan kashi 29 cikin 100 na kuri'un Kaduna a zaben 2023, zai kara samun gagarumin goyon baya a zaben 2027.
"Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga kashi 29 cikin 100 zuwa tsakanin kashi 70 da 80 cikin 100,"
In ji Uba Sani.
A zaben shugaban kasa na 2023, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya samu kuri'u 554,360 a Kaduna, yayin da Tinubu ya samu kuri'u 399,293.
Sai dai Uba Sani ya ce tsarin siyasar jihar ya sauya tun bayan zaben 2023, don haka bai dace a yi hasashen cewa sakamakon zaben 2027 zai kasance iri daya ba.

Kara karanta wannan
'Ban da Atiku,' Dan takara 1 da ya bugu kirji kan shi kadai zai iya maido tallafin mai
Sauya sheka zai taimaki APC
Uba Sani ya ce sauya shekar wasu manyan 'yan siyasa daga jam'iyyun adawa zuwa APC, musamman a Kudancin Kaduna, zai iya sauya tsarin kada kuri'a a jihar.
Vanguard ta rahoto ya ce ayyukan da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a Kaduna karkashin shugabancin Tinubu za su kara wa jam'iyyar APC karfi.
Daga cikin ayyukan da ya ambata akwai kafa Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya a Kudancin Kaduna da kuma wasu ayyukan kiwon lafiya.

Source: Original
Gwamnan ya ce yana girmama tsofaffin shugabannin jihar, ciki har da tsohon gwamna Nasir El-Rufai, Ahmed Makarfi da Namadi Sambo, amma ya ce yanzu aikinsa shi ne kare muradun APC.
Tinubu zai saukaka sufuri
A wani labarin, mun rahoto cewa shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin kara tashoshin motocin da ke amfani da iskar gas ta CNG guda 500 a fadin Najeriya.
Hakan zai kai yawan tashoshin da ake shirin samarwa karkashin shirin gwamnatin tarayya na CNG da aka kaddamar zuwa 1,000.
Tinubu ya ce gwamnatocin jihohi ma sun nuna aniyarsu ta daukar matakan rage kudin sufuri, musamman ta hanyar amfani da motocin CNG da na lantarki.
Asali: Legit.ng
