An Gaji da Allah Wadai: 'Yan Majalisa Sun Kalubalanci Tinubu kan Rashin Tsaro

An Gaji da Allah Wadai: 'Yan Majalisa Sun Kalubalanci Tinubu kan Rashin Tsaro

  • Ƙungiyar ‘yan majalisar adawa ta buƙaci Tinubu ya ɗauki matakin gaggawa kan ta’addanci, ‘yan bindiga da sace-sacen mutane a Arewacin Najeriya
  • ‘Yan majalisar sun ce hare-haren sun kai matakin da ba za a iya jurewa ba, yayin da ake kashe mutane a gidaje, gonaki da wuraren ibada
  • Sun kuma nemi a ware Dala biliyan $5 daga ajiyar kuɗin ƙasar domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga da suka addabi Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ƙungiyar ‘yan majalisar wakilan Najeriya ta bangaren adawa ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki matakin gaggawa kuma mai ƙarfi domin kawo ƙarshen ƙara ta’azzara ta’addanci.

Sun ce lallai ya kama shugaban ya kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga, kashe-kashe da sace-sacen mutane a sassan Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: Rundunar ’yan sandan Kano ta aika da gargaɗi mai zafi ga ’yan daba

Yan majalisa sun yi tir da rashin tsaro a Arewa
Wasu daga cikin yan majalisar Najeriya Hoto: House of Representatives
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa 'kungiyar ta ce yawaitar hare-haren da kuma yadda suke faruwa akai-akai ya wuce misali, musamman a Arewacin kasar nan.

Yan majalisa sun dura kan Tinubu

A ruwayar Daily Trust, sun bayyana takaici kan yadda ake kashe ‘yan Najeriya a gidajensu, gonakinsu da garuruwansu, yayin da wasu kuma ake sace su a lokacin da suke gudanar da ibada.

An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Majalisar Adawa, Fredrick Agbedi, da kakakinta, Afam Ogene, suka sanya wa hannu ranar Alhamis.

‘Yan majalisar sun buƙaci Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da wani gagarumin aikin soji mai ɗorewa wanda zai dogara da sahihan bayanan sirri, domin kwato al’ummomin da dazuzzukan da ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka suka mamaye.

Kiran yan majalisa ga Tinubu

'Yan majalisar adawa sun ce gwamnati ba za ta iya ci gaba da mayar da martani ga hare-haren ta hanyar fitar da sanarwar Allah-wadai bayan kowanne hari ba.

Kara karanta wannan

Tirkashi: APC ta dauka da zafi bayan Atiku ya yi wasu kalamai

Sun ce:

“Yawan hare-haren da kuma yadda suke maimaituwa ya kai matakin da ba za a iya jurewa ba."
Yan majalisa sun mika bukata ga Bola Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Yan majalisar sun bayyana cewa hare-haren sun raba iyalai, an sace yara daga makarantu, sannan wasu al’ummomi gaba ɗaya suka tilastawa barin gidajensu na gado.

Ƙungiyar ta kawo misalan hare-haren baya-bayan nan a wasu jihohi a matsayin shaida kan yadda matsalar tsaro ke ƙara tabarbarewa.

A Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Plateau, ta ce an kashe sama da mutane 20 a hare-haren baya-bayan nan, ciki har da mutum 23 da aka kashe a wani hari guda.

Sojoji sun fatattaki yan ta'adda

A wani labarin, kun ji cewa sojojin Operation Fansan Yamma sun kubutar da wata mata da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da ita a jihar Kebbi a yayin da aka yi aikin ceto.

Jami'an sojoji sun tarwatsa shirin karɓar kuɗin fansa, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addan tsere wa tare da barin matar a wurin, inda sojojin suka dauko ta domin sada ta da yan uwanta.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da matsa wa ’yan ta’adda da ’yan bindiga lamba, tare da kira ga jama’a su rika ba jami’an tsaro sahihan bayanai domin kawo karshen matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng