Tinubu Ya Fusata da 'Yan Bindiga Suka Sace Masallata a Neja Ya Bayar da Umarni
- Tinubu ya umarci Sojoji, ’yan sanda, DSS da sauran hukumomin tsaro su haɗa kai wajen ceto mutanen da aka sace a Jihar Neja
- ’Yan ta’adda dauke da makamai sun kutsa masallatai huɗu yayin sallar Juma’a tare da tafiya da masu ibada zuwa daji
- Shugaban ƙasa ya ce gwamnati ba za ta huta ba har sai an dawo da dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ceto masu ibada da 'yan bindiga suka sace a jihar Neja.
Shugaba Tinubu ya umarci rundunar sojojin Najeriya, ’yan sanda, hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro da leƙen asiri da abin ya shafa su ƙaddamar da aikin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar a shafinsa na X ranar Talata, 25 ga watan Agustan 2026.
Umarnin ya biyo bayan sace mutane da dama da wasu ’yan ta’adda suka yi a ranar Juma’ar da ta gabata yayin da ake gudanar da sallar Juma’a a wasu garuruwa na ƙaramar hukumar Borgu.
An sace masu ibada daga masallatai huɗu
’Yan ta’addan sun kai hari kan masallatai huɗu da ke Dekara, Kpenya, Sabon-Gida da Gidan-Zana, inda suka mamaye wuraren ibadar yayin da ake gudanar da sallar Juma’a.
Mazauna yankin sun shaida wa Daily Trust cewa maharan, waɗanda suka zo da yawa, sun shiga masallatan lokaci guda tare da kwace iko da wuraren ibadar.
Daga nan ne suka tattara da dama daga cikin masu ibadar tare da tafi da su cikin daji.
Tinubu ya nuna fushi
A cikin sanarwar, Bayo Onanuga ya bayyana cewa Tinubu ya nuna matuƙar ɓacin rai kan sacewa da kisan fararen hula marasa laifi da masu aikata laifukan suka yi.
Shugaban ya bayyana waɗanda suka kai harin a matsayin “maƙiyan zaman lafiya da maƙiyan bil’adama”, yana mai cewa ba za a bar su su tsere wa hukunci ba.
Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mutanen da aka kashe, tare da addu’ar Allah Ya jiƙansu, Ya kuma ba iyalansu ƙarfin jure wannan babban rashi.
“Ba za mu huta ba”
Tinubu ya tabbatar wa iyalan waɗanda aka sace cewa ba su kaɗai ba ne a cikin wannan mawuyacin hali.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙari har sai an dawo da ‘ya’yansu, iyayensu da sauran ’yan uwansu da aka yi garkuwa da su cikin aminci.
“Ba za mu huta ba har sai an dawo da ‘ya’yanku maza da mata, iyaye mata da ubanni gare ku cikin aminci,” in ji shi.
Ya umarci a rika ba shi rahoto
Shugaban Ƙasa ya umarci shugabannin rundunonin tsaro da su rika ba shi cikakken rahoto akai-akai kan ci gaban aikin ceto har sai an gano tare da dawo da dukkan mutanen da aka sace.
Ya kuma jaddada cewa ta’addanci ba zai tsoratar da Najeriya ba, yana mai cewa gwamnati za ta kare jama’a, al’ummomi da kuma mutuncin rayuwar ɗan Adam.
Tinubu ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta bai wa Gwamnatin Jihar Neja dukkan tallafin da ya dace domin aikin ceto, agaji da ƙarfafa matakan tsaro a yankin.

Source: Facebook
Amnesty ta yi maganar sace mutane a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Amnesty International ta yi muhimmin kira ga hukumomi kan sace masallata a Neja..
Ƙungiyar Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gaggauta tabbatar da kubutar da masallatan da aka yi garkuwa da su a wani masallaci a Jihar Neja.
Asali: Legit.ng


