Da Gaske Hafsan Tsaro Ya Bayyana a cikin Bidiyo Yana Goyon bayan ’Yan Siyasa?

Da Gaske Hafsan Tsaro Ya Bayyana a cikin Bidiyo Yana Goyon bayan ’Yan Siyasa?

  • Hedikwatar tsaron Najeriya ta yi martani game da wani bidiyo da ke yawo kan zargin Janar Olufemi Oluyede game da siyasa
  • Hedikwatar ta ce bidiyon kirkirarre ne ta amfani da fasahar AI, kuma an shirya shi ne domin ya yaudari jama’a da bata suna
  • Sojojin Najeriya sun jaddada cewa rundunar soja ƙwararriya ce, ba ta siyasa, kuma ta kuduri aniyar bin kundin tsarin mulkin ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hedikwatar Tsaron Najeriya ta yi martani kan wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta kan babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede.

Majiyoyi sun bayyana cewa an gano Oluyede a wani bidiyo yana yin kalaman da ke nuna goyon bayan siyasa.

An karyata bidiyon hasan tsaro yana goyon bayan yan siyasa
Hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, Hedikwatar Tsaron ta bayyana cewa bidiyon kirkirarre ne, kuma bai fito daga Babban Hafsan Tsaron ba.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta sake gano lam'a a shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

Sojoji sun kare hafsan tsaron Najeriya

Hedikwatar ta ce kalaman da aka danganta wa Janar Oluyede a cikin bidiyon ba gaskiya ba ne, inda ta bukaci jama’a da su yi watsi da su gaba daya.

Hedikwatar Tsaro ta bayyana babu shakka cewa bidiyon karya ne, kuma bai fito daga Babban Hafsan Tsaron Najeriya ba, kamar yadda sanarwar ta ce.

Haka kuma, Hedikwatar ta ce an kirkiri bidiyon ne ta amfani da fasahar Hankali na’ura mai kwakwalwa (AI) wajen sauya bayanai ko kirkirar sababbin bayanai, da nufin yaudarar jama’a.

Ta bayyana cewa an shirya bidiyon ne domin ya yaudari jama’a, ya karkatar da matsayar Babban Hafsan Tsaro, tare da bata sunan Rundunar Sojojin Najeriya.

Sanarwar ta ce:

“Bidiyon sakamakon amfani da fasahar Hankali na’ura mai kwakwalwa ne wajen sauya bayanai, kuma da alama an tsara shi ne domin yaudara da bata jama’a, karkatar da matsayin Babban Hafsan Tsaro, tare da jefa Rundunar Sojojin Najeriya cikin rashin kima.”

Kara karanta wannan

Abba Kabir Yusuf ya yaba wa Sheikh Jingir kan Muslim Muslim

Hedikwatar Tsaron ta kuma sake jaddada cewa Rundunar Sojojin Najeriya kungiya ce ta kwararru, wadda ba ta siyasa kuma ba ta goyon bayan kowace jam’iyyar siyasa, tare da yin aiki bisa Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya da kare kasa.

Hedikwatar ta yi Allah-wadai da kirkira da yada bidiyon na karya, tare da gargadin wadanda suka samar da shi da kuma mutanen da suke sane da hakan amma suke ci gaba da yada shi, da su daina nan take.

Hedikwatar ta bukaci ‘yan Najeriya da su rika dogaro da bayanan da Rundunar Sojojin Najeriya ke fitarwa ta kafafenta na sadarwa na hukuma kawai, tare da yin watsi da bidiyon da ke yawo.

Hafsan tsaro ya bukaci fatattakar yan ta'adda

An ji cewa babban hafsan tsaron ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya buƙaci a fatattaki ƴan ta'addan da suka takurawa ƙasar nan.

Laftanar Janar Olufemi ya umurci dakarun sojoji n kasada su nuna rashin tausayi wajen fatattakar miyagun ƴan ta'adda.

Babban hafsan sojojin ya nuna cewa ba za su lamunci abin da ya kira ƙoƙarin ƴan ta'adda na tarwatsa rayuwar ƴan Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.