2027: Rundunar ’yan Sandan Kano Ya Aika da Gargaɗi Mai Zafi ga ’yan Daba
- Kwamishinan ’yan sandan Kano ya gargadi ’yan siyasa a jihar Kano game da amfani da daba da kalaman ƙiyayya gabanin zaɓen 2027
- CP Ibrahim Bakiru ya gargadi ya buƙaci jam’iyyu da ’yan takara su guji yaɗa labaran ƙarya da tayar da hankali a kafafen sada zumunta da wajen su
- ’Yan sanda sun ce za su kama tare da gurfanar da duk wanda ya karya dokar zaɓe ko ya kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma. a jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya gargadi ’yan siyasa, jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su guji amfani da daba gabanin 2027.
Haka kuma ya ja kunnensu game da amfani da kalaman ƙiyayya, yaɗa labaran ƙarya da kuma duk wani abu da ka iya haddasa rikici yayin shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
Daily Trust ta kawo labarin cewa Bakori ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Agusta, 2026 yayin wata ganawa da shugabannin jam’iyyun siyasa da ’yan takara a Kano, wadda aka gudanar a Bompai.
Yan sanda sun zauna da yan siyasa
A ruwayar jaridar Punch, Bakori ya ce an shirya taron ne domin tabbatar da cewa harkokin siyasa da za su kai ga zaɓen 2027 sun gudana cikin lumana tare da bin tanadin doka.
Kwamishinan ya bayyana cewa yawan al’ummar Kano da muhimmancinta a siyasar ƙasar na buƙatar ’yan siyasa su kasance masu taka-tsantsan a lokacin gudanar da kamfen.
A cewarsa, idan ba a gudanar da harkokin siyasa cikin tsari ba, hakan na iya haifar da tashin hankali, tsoratar da jama’a da lalata dukiyoyi.
Shawarar yan sanda ga yan siyasa
Bakori ya buƙaci jam’iyyu da ’yan takara su guji kalaman ƙiyayya, labaran ƙarya da kuma tayar da hankali, ko a kafafen sada zumunta ko wajen su, yana mai cewa ba za a amince da tashin hankali da daba ta kowace hanya ba.

Source: Facebook
Ya kuma tunatar da su wajibcin bin tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2022 da ƙa’idojin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gindaya, ciki har da neman izinin gudanar da gangami da sauran tarukan siyasa.
Ya ce shugabannin jam’iyyu na da alhakin tabbatar da cewa magoya bayansu sun kiyaye doka tare da ɗaukar nauyin halayensu yayin harkokin siyasa.
Yan sanda sun kama dilan kwaya
A baya, kun ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani da ake zargi da safarar makamai a ƙaramar hukumar Dala tare da gano wasu miyagun makamai.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa an ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda uku da harsasai tare da karin wasu makaman.
‘Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya amsa cewa ya samo makaman ne daga jihar Katsina yayin da ya ke ci gaba da ba su bayanai a kan safarar makaman da ya ke yi.
Asali: Legit.ng

