'Ya Mana Rana': Waɗanda Tinubu Ya ba Muƙamai Sun Shirya Saka Masa a 2027
- Shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya sun fara gangamin neman goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- A wani taro a Abuja, shugabannin hukumomin sun jaddada cewa ci gaba da manufofin Tinubu zai taimaka wajen ƙarfafa nasarorin gyare-gyaren da gwamnatinsa ta fara
- Mai shirya taron, Dakta Kazeem Raji, ya ce ya kamata jami’an gwamnati su bayyana wa ’yan Najeriya irin tasirin ayyukan gwamnati, tare da neman goyon bayansu bisa doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugabannin hukumomi, ma’aikatu da wasu hukumomin gwamnati da gwamnatin tarayya sun fara shirin goyon bayan Bola Tinubu.
Masu mukaman sun naɗa sun fara wani gangami na haɗin gwiwa domin neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Source: Facebook
An bayyana hakan ne a taron farko na ƙungiyar shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya, wato Forum of PBAT CEOs, da aka gudanar a Abuja, cewar Punch.
Shugabannin hukumomin sun yi kira da a ci gaba da aiwatar da sauye-sauye da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu domin tabbatar da dorewar manufofin da aka fara.
Ƙungiyar ta ƙunshi jami’an da gwamnatin tarayya ta naɗa domin jagorantar hukumomi, sassa da hukumomin gwamnati daban-daban a ƙarƙashin ma’aikatu, sassa da hukumomi.
Shugabannin sun bayyana cewa ci gaba da manufofin gwamnati ya zama dole domin ƙarfafa nasarorin da ake samu daga sauye-sauyen da ake aiwatarwa.
Dakta Kazeem Raji, Darakta-Janar kuma Babban Darakta na hukumar NBTI, ne ya shirya taron.
Haka kuma ƙungiyar ta ambaci ilimi, gidaje, noma, kiwon lafiya, fasaha, ƙere-ƙere, wutar lantarki da haɗin intanet a matsayin wasu ɓangarorin da gwamnati ta ce ana samun ci gaba.
Raji ya ce a ƙarshe za a auna nasarar dandalin ne bisa irin sakamakon da ya samar da kuma yadda ya ƙarfafa alaƙar gwamnati da ’yan ƙasa.
Ya bukaci mambobin su kawo ƙwarewarsu, tasirinsu, hanyoyin sadarwarsu da ƙarfin hukumominsu domin cimma manufofin dandalin.
Raji ya ce:
“Mai girma Shugaban ƙasa ya ba mu amanar aiki. Mu ba shi mafi kyawun abin da muke da shi, ya damƙa mana nauyi. Mu rama wannan amana ta hanyar nuna ƙwarewa da samar da sakamako."

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: ICPC ta gano sunayen manyan jami'ai 4 da suka taimaka wajen kafa hukumar bogi
Ya bukaci shugabannin hukumomin su ɗauki alhakin bayyana nasarorin gwamnati ta hanyar samar da hujjojin tasirin ayyukan hukumominsu.
Gwamnatin Tinubu ta aiwatar da manyan sauye-sauyen tattalin arziki tun bayan hawanta mulki, ciki har da cire tallafin man fetur da sauya tsarin tafiyar da harkokin musayar kuɗin waje.
Haka kuma gwamnati ta aiwatar da sauye-sauyen kuɗaɗen shiga da haraji, yayin da take cewa matakan sun taimaka wajen inganta zuba jari, kuɗaɗen shiga da ababen more rayuwa.
Sai dai sauye-sauyen sun fuskanci suka saboda hauhawar farashi da kuma yadda suka shafi tsadar rayuwa ga ’yan Najeriya.
Malaman Musulunci 500 sun goyi bayan Tinubu
An ji cewa Malaman addinin Musulunci da shugabannin siyasa sama da 500 sun amince da sake zaben Shugaba Bola Tinubu.
An bayyana hakan ne yayin wani taron JIBWIS a Jos, inda mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Jibril Barau ya halarta.
JIBWIS ta kuma jaddada muhimmancin gaskiya, kwarewa, adalci da rikon amana, tare da yin kira da a inganta tsaro.
Asali: Legit.ng
