Bayan Korafi kan Kudin Tallafin Mai, Tinubu Ya Fara Raba Motocin Lantarki
- Gwamnatin tarayya ta sanar da isowar rukunin farko na motocin lantarki da za a raba wa ma’aikatan gwamnati a Najeriya
- Hukumar NADDC ta ce shirin zai taimaka wajen inganta amfani da makamashi mai tsafta da kuma rage kuɗin sufuri ga 'yan kasa
- Shugaban hukumar ya ce gwamnati ta kuma samar da kayayyakin more rayuwar motocin lantarki a jami’o’i 16 a fadin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta sanar da isowar rukunin farko na motocin lantarki da ta yi alkawarin samarwa ma’aikatan gwamnati, a wani mataki na inganta amfani da makamashi mai tsafta da rage tsadar sufuri.
Shugaban hukumar raya sufuri ta NADDC, Joseph Osanipin, ya bayyana hakan ne bayan ganawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Source: Twitter
Punch ta rahoto cewa Osanipin ya ce isowar motocin ya nuna fara aiwatar da shirin gwamnatin tarayya na fadada amfani da motocin lantarki tare da samar da kayayyakin more rayuwa da za su tallafa wa tsarin.
An fara raba motocin lantarki
Osanipin ya ce motocin da aka kawo a rukunin farko dukkansu motocin lantarki ne, kuma wannan shi ne farkon karin motocin da gwamnati za ta samar.
Ya ce:
"A yau kun ji a labarai cewa an kawo rukunin farko na motocin da shugaban kasa ya yi wa ma’aikatan gwamnati alkawari, kuma dukkansu motocin lantarki ne.
"Wannan shi ne farkon karin motocin da za su ci gaba da zuwa."
Ya ce gwamnati ta kuma samar da wasu kayayyakin tallafa wa motocin lantarki a kusan jami’o’i 16 a fadin Najeriya domin taimakawa wajen gina tsarin amfani da irin motocin.
Batun bunkasa amfani da CNG
Shugaban NADDC ya ce sauya tsarin amfani da fetur zuwa makamashi irin su gas da lantarki ba zai yi tasiri cikin gaggawa ba, domin ana bukatar zuba jari wajen samar da tashoshin cike gas, na'urorin cike gas da sauransu.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya shirya dawo da litar fetur N200 a Najeriya
Ya bayyana cewa adadin kamfanonin da ke da lasisin sayar da gas ya karu daga kusan guda hudu zuwa 81, wanda ya ce hakan na nuna yadda masu zaman kansu ke kara shiga shirin gwamnatin na bunkasa amfani da CNG.
Osanipin ya ce wasu mutane sun fara cin gajiyar tsarin, inda ya ba da misalin wani matafiyi da ya ce kudin man da yake kashewa ya sauka daga sama da N200,000 zuwa kusan N40,000 bayan ya koma amfani da CNG.

Source: Facebook
Sanata John Enoh ya wallafa hotunan motocin da aka raba a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce ya halarci wajen.
Gwamnoni za su bunkasa sufuri
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnoni 36 na jihohin Najeriya sun amince da yin aiki kan hanyoyin bunkasa samar da kudi da kuma fadada amfani da motocin CNG.
Gwamnonin sun ce za su hada kai da masu zaman kansu domin kara zuba jari wajen samar da CNG da kayayyakin da ake bukata domin fadada amfani da shi.
An ce manufar shirin ita ce rage tsadar sufuri, wanda ake sa ran zai taimaka wajen rage farashin kayayyaki da ayyuka a Najeriya.
Asali: Legit.ng
