Asiri Ya Tonu: ICPC Ta Gano Sunayen Manyan Jami'ai 4 da Suka Taimaka Wajen Kafa Hukumar Bogi

Asiri Ya Tonu: ICPC Ta Gano Sunayen Manyan Jami'ai 4 da Suka Taimaka Wajen Kafa Hukumar Bogi

  • Hukumar ICPC ta gano cewa wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya hudu sun taimaka wa Adeniyi Adeyemi, shugaban hukumar bogi ya PFIPC
  • Binciken ya nuna cewa an ba hukumar lambar gudanarwa, matsayin gudanar da kuɗaɗe da kuma damar shiga wasu tsare-tsaren gwamnati
  • Haka kuma, hukumar ICPC ta gano zargin biyan wata ma’aikaciyar gwamnati daga cikin wadanda ake zargi N500,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Yaki da Rashaws ta ICPC ta gano yadda wasu manyan jami'an gwamnatin tarayya suka taimaka wajen kirkiro hukumar bogi ta PFIPC.

Rahoton wucin-gadi na binciken ICPC kan lamarin PFIPC ne ya bayyana hakan, inda ya ce jami'sn sun takmaka wa Adeniyi Adeyemi, wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban hukumar ta bogi.

Shugaban hukumar bogi.
Shugaban hukumar bogi da ake ta surutu a kanta a Najeriya, Adeniyi Adeyemi
Source: Facebook

Ta yaya PFIPC ta samu amincewa?

Premium Times ta rahoto cewa s binciken ICPC, Adeyemi ya fara neman a amince da ƙungiyar a hukumance a cikin tsarin gwamnati ne a watan Nuwamba 2024.

Kara karanta wannan

An taso gwamnoni a gaba bayan FAAC ta cika aljihunsu da N47tr

Ya tuntubi Ofishin Akanta-Janar na Tarayya (OAGF) domin neman lambar gudanarwa, matsayin gudanar da kuɗaɗenta da kuma izinin buɗe asusu a Babban Bankin Najeriya (CBN).

Ya gabatar da wasu takardu da ake zargin duk na bogi ne, inda a ranar 27 ga Mayu 2025, OAGF ya bai wa ƙungiyar matsayin gudanar da kuɗaɗenta da kanta tare da ba ta lambar gudanarwa ta 0111062001.

Wannan amincewa ta ba PFIPC damar shiga cikin kasafin kuɗin gwamnatin tarayya na 2026 tare da samun damar shiga wasu tsare-tsaren kuɗaɗen gwamnati.

Waɗanne ma’aikata suka taimaka?

Binciken ICPC ya duba rawar da wasu ma’aikatan gwamnati uku suka taka wajen samun izinin kafa hukumar bogin da ɗaukar ma’aikata na PFIPC.

Sun hada da Rose Achem, babbar jami’ar gudanarwa ga Darakta-Janar na Ofishin Kasafin Kuɗin Tarayya; da Patricia Akhigbe, mataimakiyar darakta a Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi.

Ta ukun ita ce Mimi Abu, daraktar tsara tsarin hukumomi da bunƙasa su a Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (OHCSF).

Kara karanta wannan

Hukumar bogi: Dalilin ICPC na tsame sunan Gbajabiamila daga kafa PFIPC

A cewar ICPC, Achem ce ta gabatar da Akhigbe ga Abu a matsayin shugabar sashen kula da ma’aikata na PFIPC, duk da cewa Akhigbe mataimakiyar darakta ce a Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi.

ICPC ta gano cewa Achem, Akhigbe da Abu sun taimaka wajen samun amincewar ta hannun OHCSF, inda aka gano cewa Adeyemi ya bai wa Akhigbe N500,000 a lokacin bikin Easter na 2025.

Ta yaya Adeyemi ya samu ofis?

ICPC ta kuma binciki rawar Aminu Abdullahi, jami’in da ke kula da rabon ofisoshi a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF), kamar yadda Punch ta ruwaito.

A cewar binciken, Ibrahim Abdulkadir, mataimakin darakta a General Services, ne ya haɗa Abdullahi da Adeyemi a watan Maris 2025.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

ICPC ta gano cewa Abdullahi ya ware wa PFIPC ofisoshin da tsohon hadimin shugaban kasa, Doyin Salami, ya taɓa amfani da su a Federal Secretariat Phase III domin amfani na wucin-gadi ba tare da rubutacciyar amincewa ba.

Binciken bayanan asusun bankin Abdullahi ya nuna cewa ya karɓi N3.25m daga Adeyemi a kashi uku tsakanin watan Maris da Nuwamba 2025, a cewar ICPC.

Tinubu ya fusata bayan gano hukumar bogi

Kara karanta wannan

Binciken ICPC ya tono yadda hukumar bogi ta shiga kasafin kudin Najeriya

A wni labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci a gaggauta kama Prince George Buchi Nwabueze bayan gano wata hukuma da ake zargin ta bogi ce.

An dakatar da manyan sakatarorin gwamnatin tarayya guda uku sakamakon binciken da aka gudanar kan wannan hukuma guda ta bogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262