Danjuma La’ah ya doke Bala Bentex a akwatin cikin Garin Manchok

Danjuma La’ah ya doke Bala Bentex a akwatin cikin Garin Manchok

Mun samu labari daga jaridar Daily Trust cewa Barnabas Bantex, wanda shi ne mataimakin gwamnan jihar Kaduna ya rasa akwatin yankin sa na cikin Garin Manchok a hannun jam’iyyar PDP.

Danjuma La’ah ya doke Bala Bentex a akwatin cikin Garin Manchok
Bala Bentex ya sha kashi a hannun Danjuma La’ah na PDP
Asali: UGC

Arch. Barnabas Bantex ya samu kuri’a 2113, yayin da shi kuma ‘dan takarar PDP wanda shi ne yake kan mulki ya samu kuri’u 2, 301. Malamin zaben yankin watau Yusuf Emmanuel shi ne wanda ya sanar da wannan sakamakon.

Manema labarai dai sun kawo labari cewa Bala Bantex ya lashe akwatin da yake zabe da kuri’a 227 inda ‘dan takarar PDP ya iya samun 15 kacal. Sai dai bayan an hada kuri’ar yankin gaba daya, APC ta sha kaye a hannun 'Dan PDP.

KU KARANTA: Sakamakon zaben shugaban kasa da kuma Majalisa daga Jihar Kaduna

A zaben shugaban kasa kuma shugaba Muhammadu Buhari na APC ya samu kuri’a 1, 443 inda shi kuma Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta PDP ya tashi da kuri’a 2, 991. Yanzu mu na cigaba da jiran sakamakon yankin.

Yanzu haka dai Sanata Danjuma La’ah ne yake kan kujerar inda yake neman komawa majalisar dattawa domin ya wakilci Mazabar Kudancin Kaduna. Kusan dai ba a samun wanda yake yin tazarce a wannan kujera a Kaduna.

A zaben majalisar tarayya, PDP ta samu 2,056 yayin da APC ta samu kuri’a 1,641. Jam’iyyar UPN ta samu 243, PRP 191 sai kuma jam’iyyar adawa ta SDP ta iya tara kuri’a 50. Ana cigaba da kirga zaben jiya a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel