2027: Pantami Ka Iya Goyon bayan Tinubu a Kaikaice saboda Tasirin Wike a Sama

2027: Pantami Ka Iya Goyon bayan Tinubu a Kaikaice saboda Tasirin Wike a Sama

  • Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Pantami, ya koma PDP a Gombe, tare da goyon bayan kungiyar Rainbow Coalition
  • Wannan sauyi na nufin Pantami ka iya mara wa Shugaba Tinubu baya wajen neman wa’adin mulki na biyu, yayin da yake adawa da APC
  • Matakin ya bayyana yadda shirye-shiryen Rainbow Coalition a jihohi ke cike da al’amura masu sarkakiya da ra’ayoyi masu karo da juna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Pantami, Gombe - A Jihar Gombe, tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Pantami, ya koma PDP tare da goyon bayan kungiyar Rainbow Coalition.

Wannan sauyi na nufin zai mara wa Shugaba Tinubu baya wajen neman sake lashe zabe, yayin da yake aiki don ganin dan takarar gwamnan APC bai yi nasara ba.

Kara karanta wannan

'Ni na ci zaɓe a 2023': Kalaman Obi da suka dugunzuma fadar shugaban ƙasa

Siyasar Gombe za ta sauya salo da ake zargin Pantami zai iya goyon bayan Tinubu
Isa Ali Pantami, Bola Tinubu da Nyesom Wike. Hoto: Professor Isa Ali Pantami, Nyesom Ezenwo Wike.
Source: Facebook

Hakan ya nuna yadda tsarin Rainbow Coalition a matakin jihohi ke kunshe da shirye-shirye masu sarkakiya, inda wasu manufofi ke sabawa da juna, cewar Vanguard.

Yadda matsala ke neman shiga Rainbow Coalition

Wasu manyan bangarori masu karfi a jam’iyyar APC mai mulki sun yi fatali da Rainbow Coalition da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya jagoranta.

Bangarorin sun ce Rainbow Coalition ba wai kawai zai cutar da ‘yan takarar APC a zaben 2027 ba, har ma zai iya kawo cikas ga yunkurin Shugaba Bola Tinubu na neman sake lashe zabe.

Wike, wanda ake kallonsa a matsayin mai fada-a-ji a bangaren PDP da INEC ta amince da shi, ya dage cewa Rainbow Coalition na goyon bayan Tinubu dari bisa dari.

Wike ya ce masu adawa da shi sun mayar da hankali wajen yakarsa ne saboda goyon bayan da yake bai wa Shugaba Tinubu, cewar Punch.

Sai dai abokan hamayyarsa sun mayar da martani cewa tsayar da ‘yan takara daga jam’iyyu daban-daban karkashin Rainbow Coalition na iya jefa masu kada kuri’a, musamman wadanda ke yankunan karkara, cikin rudani a ranar zabe.

Kara karanta wannan

Rigimar El Rufai da ministan tsaro: Jama'atu Nasril Islam da CAN sun tsoma baki

Tuni dai wannan rikici ya fara haifar da cece-ku-ce a jihohi da dama, ciki har da Rivers, Kwara, Gombe da Cross River.

Wike ya ce Gwamnan Imo, Sanata Hope Uzodimma, da Gwamnan Kwara kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, AbdulRahman AbdulRazaq, na kan gaba wajen yaki da shi.

Kungiyar Wike da ke PDP za ta goyi bayan Tinubu
Ministan Abuja, Nyesom Wike da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Lere Olayinka, Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Pantami ka iya goyon bayan Tinubu

Duk da kasancewarsa dan jam'iyyar PDP wanda ke adawa da jam'iyyar APC da Gwamna Inuwa Yahaya a Gombe, Isa Pantami ka iya marawa Bola Tinubu baya a 2027.

Wannan na zuwa ne bayan samun takara a PDP da ake zargin ya samu goyon bayan kungiyar wacce ke karkashin Wike.

Har ila yau, Wike wanda dan jam'iyyar PDP ne amma yana rike da mukamin ministan Abuja kuma balo-balo ya ce zai goyi bayan tazarcen Tinubu da ke APC.

Pantami ya bugi kirji kan zaɓen gwamnan Gombe

Mun ba ku labarin cewa dan takarar jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar cewa zai lashe zaben gwamna a 2027.

A wata hira da ya yi, Pantami ya bayyana cewa babu alamar jin tsoro ko dardar a takarar da ya ke yi kuma zai fuskanci dukkan kalubalen jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.