Sanata Ndume Ya Bayyana Mutane 3 da Suka Cece Shi da Aka So Kwarfe Shi a APC

Sanata Ndume Ya Bayyana Mutane 3 da Suka Cece Shi da Aka So Kwarfe Shi a APC

  • Sanata Ndume ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya dage kan a saka sunansa cikin jerin ‘yan takarar APC na majalisar dattawa
  • Ali Ndume ya ce akwai wasu manyan mutane sun nuna goyon baya wajen tabbatar da komawarsa takara a zaben 2027 da ake tunkara
  • Ndume ya bukaci shugabannin APC na Gwoza su koma mazabunsu su kara karfafa gangamin neman kuri’u gabanin zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Sanata Mohammed Ali Ndume ya bayyana mutanen da suka taimaka masa wajen sake samun tikitin jam'iyyar APC.

Sanata Ndume ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da komawarsa takarar Sanata a 2027.

Ndume ya ce Tinubu ya cece shi
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume Hoto: Senator Muhammad Ali Ndume
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce Sanata Ndume ya bayyana hakan ne ranar Talata, 25 ga watan Agustan 2026 lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin jam’iyyar APC na Karamar Hukumar Gwoza a gidansa da ke Maiduguri.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gamu da matsala har a majalisa daga nadin kwamitin yakin neman zabe

Shugabannin jam’iyyar sun kai masa ziyara ne domin taya shi murnar samun tikitin APC na sake neman kujerar Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a zaben 2027.

Tinubu ya dage kan saka sunan Ndume

Ndume ya bayyana samun tikitin a matsayin kaddarar Allah, yana mai cewa duk da cewa mutane na iya tsara abubuwa, ikon karshe da makomar dan Adam suna hannun Allah.

Ya bayyana cewa da farko an cire sunansa daga jerin sunayen da aka gabatar domin tantance ‘yan takarar kujerun Sanata na APC.

Sai dai ya ce Shugaba Tinubu ya dage cewa dole a mayar da sunansa cikin jerin wadanda za a yi la’akari da su.

“An kai wa Shugaban Kasa sunayen wadanda ake son su samu tikitin APC a tsakaninmu sanatoci, amma ba a saka sunana ba. Shugaban Kasa ya dage cewa a koma a saka sunana,” in ji Ndume.

Ndume ya yaba wa Zulum da Oluremi Tinubu

Kara karanta wannan

Duk da suna jam'iyya 1, Gwamna Radda ya yi maganar nadin da Tinubu ya yi maaa a kwamitin kamfen

Sanatan ya ce kafin lokaci ya kure, Gwamna Zulum shi ma ya je fadar shugaban kasa domin nuna goyon bayansa ga a saka sunansa.

Ndume ya kuma bayyana cewa Sanata Oluremi Tinubu ta nuna irin wannan goyon baya wajen tabbatar da cewa an yi la’akari da sunansa.

Ya gode wa Shugaba Tinubu, Gwamna Zulum da Uwargidan Shugaban Kasa bisa goyon bayan da suka nuna masa, yana mai cewa ba zai dauki irin wannan taimako da wasa ba.

Ndume ya nemi a kara samar da ayyukan hanya

Ndume ya kuma bayyana cewa ya ci gaba da tattaunawa da Shugaba Tinubu kan wasu muhimman ayyukan raya kasa da suka hada da hanyoyin Biu–Gombe da Ngala–Dikwa.

Ya ce Shugaban Kasa ya nuna kyakkyawar fahimta game da bukatar inganta hanyoyin, yana mai cewa al’ummar Borno na da alhakin nuna godiya ga irin kulawar da aka bai wa jihar da shiyyar Arewa maso Gabas.

Sanatan ya kuma bukaci al’ummar yankin su nuna goyon baya ga Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, wanda ya bayyana a matsayin dan yankinsu, ta hanyar tabbatar da nasarar APC a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 6, malaman addini 500 sun bayyana dan takarar shugaban kasarsu a 2027

Ndume ya yabi Shugaba Tinubu
Sanata Ali Ndume a zauren majalisar dattawa Hoto: Senator Muhammad Ali Ndume
Source: Facebook

Ndume ya soki hadiman Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Ali Ndume, mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya soki wasu daga cikin hadimai na kusa da Shugaba Bola Tinubu.

Ali Ndume ya yi zargin cewa shugaban kasa yana samun shawarwari marasa kyau daga masu ba shi shawara wadanda ba su fahimci siyasa ko sanin halin da talakawa ke ciki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng