Babban Ɗan Marigayi MKO Abiola Ya Shiga Siyasa, Ya Bayyana Gyara Na Farko Da Zai Kawo

Babban Ɗan Marigayi MKO Abiola Ya Shiga Siyasa, Ya Bayyana Gyara Na Farko Da Zai Kawo

  • Dan Marigayi Cif MKO Abiola, Kola Abiola ya shiga siyasa ya kuma zabi jam'iyyar Peoples Redemption Party, PRP
  • Kola, wanda Shugaban jam'iyyar PRP na kasa Bello Falalu ya tarba a Abuja ya ce ya zabi PRP ne don itace jam'iyya ta al'umma
  • Ya kuma ce abin farko da zai fara yi shine wayar da kan matasa su shiga siyasa a rika damawa da su kuma su dena siyasan uban gida

FCT, Abuja - Mr Kola Abiola, babban dan wanda ake yi wa kallon ya lashe zaben shugaban kasa na June 12, marigayi Cif MKO Abiola ya shiga jam'iyyar Peoples Redemption Party, PRP, rahoton The Nation.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya rahoto cewa Shugaban PRP na kasa, Bello Falalu, ya karbi Abiola a jam'iyyar ta PRP a hukumance a sakatariyar jam'iyyar na kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Matsaloli ta ko ina: Najeriya na bukatar shugabanni masu tsoron Allah, inji malamin addini

Babban Ɗan Marigayi MKO Abiola, Ya Shiga Jam'iyyar Siyasa
Babban Ɗan Marigayi MKO Abiola, Ya Shiga Jam'iyyar PRP. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

"Ina maka maraba zuwa jam'iyyar mu a hukumance. Abubuwan da ka yi a baya ba boyayyu bane," a cewar Bello yayin maraba da Abiola.

Tunda farko, Abiola ya ce:

"Yau ne ranar farko na dawowa na siyasa, bayan barinta tsawon shekaru 27.
" Na zabi in shiga PRP ne saboda wasu dalilai masu muhimmanci.
"Na duba tarihin Najeriya don ganin jam'iyyar da ke wakiltar Najeriya.
"Na koma baya na yi bincike kuma na gano PRP ce jam'iyya mafi tsufa; har yanzu tana da akidu na demokradiyya da yadda ya kamata Najeriya ta kasance."

A cewarsa, jam'iyya ce wacce wanda mutane suka kafa ta domin mutane kamar yadda The Punch ta rahoto.

Kola ya yi kira ga matasa su shiga siyasa a dama da su

Kara karanta wannan

Osinbajo: Idan Tinubu ya kawo ka siyasa, ka janye niyyar takarar Shugaban kasa – Jigon APC

A yayin da ya ke magana kan karancin matasa a siyasa, ya ce,

"Muna da dimbin matasa amma ba a damawa da su, a harkar siyasa.
"Abin farko da na ke son yi shine kawo canji a harkar siyasar, in kawar da hankulan matasa daga siyasar uban gida.
"Hanyar da za a cimma haka shine bawa ainihin wadanda ke da Najeriya, masu shekaru 18 zuwa 36, da sune kashi 75 cikin 100, damar fada a ji ta hanyar amfani da yawansu."

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Kara karanta wannan

Na cancanci gaje kujerar Buhari: Inji Amaechi ga jama'ar Katsina yayin wata ziyara

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel