Hadimin Tinubu da gwamnan Yobe sun ba Izalar Jingir Naira miliyan 600

Hadimin Tinubu da gwamnan Yobe sun ba Izalar Jingir Naira miliyan 600

  • Gwamnan Yobe da mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Kabiru Ibrahim Masari, sun yi alkawarin ba da N600m ga Izala
  • An ce za a yi amfani da kudin wajen ci gaba da aikin gina jami'ar Fortune da kungiyar JIBWIS ke ginawa a Magama Gumau da ke jihar Bauchi
  • Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bukaci Musulmi da sauran masu hannu da shuni su bayar da gudunmawa domin kammala gina jami'ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau – Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, da Babban Mai Bai wa Shugaba Bola Tinubu Shawara kan Harkokin Siyasa, Kabiru Ibrahim Masari, sun yi alkawarin bayar da N600m domin aikin gina jami'ar Fortune.

Ana cigaba da gina jami'ar Izala mai suna Fortune garin Magama Gumau da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi da ke Najeriya.

Kara karanta wannan

Sanata Barau yi fito da me Sheikh Jingir ke nufi da Muslim Muslim

Taron Izala a Jos
Sheikh Jingir da wasu 'yan siyasa a wajen taron Izala a Jos. Hoto: Ibrahim Maina Muhammad
Source: Facebook

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa Masari da Gwamna Buni sun sanar da bayar da gudunmawar ne yayin wani taron kasa na yini guda da kungiyar JIBWIS ta shirya a birnin Jos.

Miliyoyin da za a ba Izala

A wajen taron da Izala ta yi, Kabiru Masari ya ce bai sani ba cewa kungiyar JIBWIS tana da irin wannan babban aikin gina jami'a da ake gudanarwa.

Masari ya ce ya yi alkawarin bayar da N300m domin taimakawa wajen ci gaba da aikin, yayin da shi ma Gwamna Mai Mala Buni ya yi alkawarin bayar da N300m.

Ya ce:

“Ban san cewa kungiyar tana da irin wannan aiki da ake gudanarwa ba. Na yi alkawarin bayar da N300m, sannan Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe shi ma ya yi alkawarin bayar da N300m domin aikin.”

Kiran da Sheikh Jingir ya yi

Tun da farko, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga Musulmi da sauran masu hannu da shuni a Najeriya su bayar da gudunmawa domin kammala aikin gina jami'ar Fortune.

Kara karanta wannan

Duniya labari: Babban malamin Musulunci kuma shugaban JIBWIS ya rasu

Sheikh Jingir ya bayyana cewa jami'ar ba mallakinsa ba ce, illa wata cibiyar ilimi ce ta kungiyar JIBWIS da za ta amfani al'umma.

Ya ce idan aka kammala gina jami'ar, ba Musulmi kadai za su amfana da ita ba, har ma da Kiristoci da sauran 'yan Najeriya.

Malamin ya kuma bukaci wasu 'yan siyasa da masu hannu da shuni da suka taba yin alkawarin bayar da gudunmawa su cika alkawuran da suka dauka.

Jami'ar da Izala ke ginawa
Wajen da ake aikin gina jami'ar Fortune ta Izala. Hoto: Ibrahim Maina Muhammad
Source: Facebook

Ya ambaci Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, da Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, wadanda a baya suka yi alkawarin bayar da N450m da N300m.

Ga bidiyon bayar da kudin da Abubakar Yunusa ya wallafa a X:

Maganar Jingir kan Kiristoci

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban majalisar malaman kungiyar JIBWIS, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya karyata zargin cewa yana kin Kiristoci.

Sheikh Jingir ya ce kalaman da wasu suka danganta da shi bayan wani taron daurin auren gata a jihar Kano an yi masu mummunar fahimta.

Ya bayyana cewa addinin Musulunci yana koyar da adalci da kyautatawa mutane ba tare da la'akari da addininsu ko bangarensu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng