Sanata Barau Ya Fito da Me Sheikh Jingir ke Nufi da Muslim Muslim
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya yaba wa Sheikh Sani Yahaya Jingir kan irin gudunmawar da yake bayarwa
- Barau ya ce manufar Sheikh Jingir wajen tallata Muslim Muslim neman haɗin kai da tabbatar da adalci da zaman lafiya a Najeriya ne
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ya bayyana hakan ne yayin taron da Izala ta shirya a Jos, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato – Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya yaba wa shugaban malaman Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, kan aikin da yake yi wa addini da al'umma.
Barau ya bayyana hakan ne yayin da ya halarci taron muhawara na ƙasa na yini ɗaya da JIBWIS ta shirya a birnin Jos, jihar Plateau.

Source: Facebook
Sanata Barau ya wallafa a Facebook cewa taron ya mayar da hankali kan ƙarfafa siyasa mai ma'ana da tabbatar da adalci domin samun haɗin kai da ci gaban Najeriya.
Barau Jibrin ya yaba wa Sheikh Jingir
A yayin jawabin da ya gabatar a taron, Barau Jibrin ya yi godiya ta musamman ga Sheikh Jingir kan gudunmawar da yake bayarwa wajen addini da kuma ci gaban al'umma.
A bidiyon da Ibrahim Maina ya wallafa a Facebook, Barau ya ce ba kowa ne zai fahimci manufofin Sheikh Jingir ba sai wanda ya yi nazari sosai kan batun siyasar Najeriya.
Barau ya ce kiran da Sheikh Jingir yake yi kan batun "Muslim-Muslim" ba wai saboda yana yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kamfen ba ne, illa saboda yana son ganin an samu haɗin kai da fahimtar juna a ƙasa.
Manufar Jingir ita ce zaman lafiya
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ya bayyana cewa babban abin da Sheikh Jingir yake nema shi ne Najeriya ta zauna lafiya, tare da tabbatar da adalci da zaman lafiya tsakanin 'yan ƙasa.
Ya ce malamin yana son ganin an ɗaukaka ƙimar Musulunci tare da ci gaba da kira ga shugabanni da al'umma su tabbatar da adalci.

Source: Facebook
Kiran Barau kan hada kai
Barau ya kuma yi magana kan muhimmancin haɗin kan ƙasa, adalci da kuma shiga harkokin siyasa saboda kishin ƙasa.
Sanatan ya ce shugabanci nagari da siyasa mai ma'ana na daga cikin hanyoyin da za a iya samun zaman lafiya da ci gaban Najeriya.
Ya bayyana godiyarsa ga masu shirya taron bisa samar da wani muhimmin dandali na tattaunawa kan matsalolin da ke addabar ƙasa.
Ya ce ta hanyar haɗin kai, adalci, shugabanci na gari da kuma shiga siyasa cikin tsari, Najeriya za ta iya samun ƙarin zaman lafiya da ci gaba.
Jingir ya musanta ƙin Kiristoci
A wani labarin, mun ruwaito cewa Sheikh Sani Yahaya Jingir ya musanta zargin cewa baya son Kiristoci, yana mai cewa kalaman da ya yi a baya an fahimce su ba daidai ba.
Jingir ya ce zargin cewa baya son Kiristoci ƙarya ce, yana mai cewa Musulunci yana koyar da soyayya da adalci ga mutane masu addinai daban-daban.
Ya ce Musulmai za su kasance masu alhakin duk wani zalunci da suka aikata wa waɗanda ba Musulmai ba, yana mai jaddada cewa adalci ya shafi kowa ba tare da la'akari da addininsa ba.
Asali: Legit.ng

