Shugaban APC Ya Sauka a Kano, Ya Yi Ganawar Sirri da Sarki Sanusi II

Shugaban APC Ya Sauka a Kano, Ya Yi Ganawar Sirri da Sarki Sanusi II

  • Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai wa Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ziyarar ban girma a fadarsa
  • Yilwatda da Khalifa Muhammadu Sanusi II sun gudanar da ganawar sirri bayan Sarkin Kano ya dawo daga babban birnin tarayya Abuja
  • Wannan muhimmiyar gana wa ta zo ne a lokacin da ake ci gaba da dambarwa game da sarautar Kano, duk da dai zafin adawa ya ragu game da kujerar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai wa Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ziyarar ban girma a fadarsa.

An gudanar da ziyarar ne ranar Asabar, 22 ga watan Agusta, 2026, a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar hankali gabanin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Bayan kalaman Wike, NDC ta fadi yadda ta shirya kwace Abuja a 2027

Shugaban APC ya ziyarci jihar Kano
Nentawe Yilwatda tare da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
Source: UGC

Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan gana wa an yi ta ne a sirri, yayin da batun ke zuwa kwanaki kadan bayan an kafa kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu.

Shugaban APC da Sarkin Kano sun gana

Politics Nigeria ta kawo labari cewa wani na kusa da Sarkin Kano, Muhammad Dallatu, ya tabbatar da ziyarar ranar Lahadi, 2 ga watan Agusta, 2026.

Ya bayar da tabbacin cewa an yi tattaunwar sirrin tsakanin jagororin jim kaɗan bayan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya dawo daga Abuja.

Dallatu ya ce:

"Shugaban APC na kasa ya kawo ziyarar ban girma ga Sarkin Kano a fadarsa a ranar Asabar."

Ya ƙara da cewa:

“Sarkin ya dawo daga Abuja ne a lokacin da aka yi tattaunawar, kuma an yi ganawar a sirrance."

Abin da Sarki da Shugaban APC suka tattauna

A cewar Dallatu, ganawar ta kasance ta sirri, don haka ba zai iya bayyana batutuwan da aka tattauna tsakanin Sarki Sanusi da shugaban APC na ƙasa ba.

Kara karanta wannan

Rasuwar babban jigon APC a Kano ta taɓa Shugaba Tinubu ana shirin fara kamfen 2027

Ya ce:

"An yi ganawar a sirrance, saboda haka ba zan iya bayyana abubuwan da Mai martaba Sarki da shugaban APC suka yi magana a kai ba."

Ziyarar ta zo ne a yayin da ake ci gaba da takaddamar sarautar Kano, wadda ta dade tana raba kan wasu masu ruwa da tsaki na siyasa da na masarautar jihar.

Takaddamar ta samo asali ne daga matakin gwamnatin tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, a shekarar 2019, na raba masarautar Kano zuwa masarautu biyar.

A wancan lokacin, an cire Sanusi daga sarautar Kano, yayin da aka naɗa Aminu Ado Bayero a matsayin sarki na 15. Lamarin ya haifar da babbar takaddama ta siyasa da masarauta.

Sai dai a shekarar 2024, gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta soke dokar da ta kafa masarautun biyar, tare da dawo da masarautar Kano ƙarƙashin Sanusi.

Duk da haka, matakin bai kawo ƙarshen rikicin ba, domin Bayero ya ci gaba da samun goyon bayan wasu masu ruwa da tsaki na siyasa da na gargajiya, musamman waɗanda ke da alaƙa da gwamnatin Ganduje.

Kara karanta wannan

APC, ADC da jam'iyyun da suka bayyana shirinsu na fara yakin neman zaben shugaban kasa

Sarkin Kano ya yi magana kan 2027

A baya, kun ji cewa Masarautar Kano da malaman addinin Musulunci sun hango abin da ya dace yan Najeriya su yi gabanin babban zaben 2027 mai zuwa da tsaro.

Shugabannin addini sun ce tarbiyyar yara bisa koyarwar Alƙur’ani na da muhimmiyar rawa wajen samar da al’umma mai zaman lafiya da ɗorewar tsaro.

Sun kuma yi kira ga waɗanda suka kammala karatun Alƙur’ani da su zama jakadu na zaman lafiya, haƙuri da kyawawan ɗabi’u a cikin al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng