Kano: An Gabatar da Kudurin Gaggawa a Majalisa bayan Mutuwar Yara 50
- Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci Gwamna Abba Yusuf ya gaggauta daukar matakan dakile cutar diphtheria da ta hallaka yara da dama
- 'Dan majalisa, Ibrahim Muhammad, ya ce cutar ta yadu zuwa wasu al’ummomi a karamar hukumar Kiru, inda wani shugaban matasan APC ya rasa ‘ya’ya biyu a rana guda
- Majalisar ta umarci kwamitinta mai kula da lafiya da ya tuntubi Ma’aikatar Lafiya kan aiwatar da dokar kare lafiya da kuma samar da agajin gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gaggauta daukar matakan dakile barkewar cutar mashako wato 'diphteria' da ake zargin ta hallaka sama da yara 50 a karamar hukumar Rano.

Kara karanta wannan
Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah
Majalisar ta yi wannan kiran ne yayin zaman majalisar na ranar Litinin, 24 ga watan Agusta,2026 bayan dan majalisar da ke wakiltar mazabar Rano, Ibrahim Muhammad, ya gabatar da kudirin neman daukar matakin gaggawa kan lamarin.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa a yayin gabatar da kudirin, Ibrahim Muhammad ya ce cutar ta fi kamari a yankunan Ridin da Sabuwar Kaura na karamar hukumar Rano, inda ta yi sanadin mutuwar sama da yara 50.
Ana bukatar matakin gaggawa a Kano
A ruwayar Channels TV, 'Dan majalisar ya ce duk da cewa an riga an dauki wasu matakan gaggawa, da suka hada da sayen magunguna da tura ma’aikatan lafiya zuwa al’ummomin da cutar ta shafa, har yanzu ana bukatar karin dauki domin dakile yaduwar cutar.
A kalamansa:
“Ko da yake an dauki matakan gaggawa, daga ciki har da sayen magunguna da tura ma’aikatan lafiya zuwa al’ummomin da abin ya shafa, ana bukatar karin dauki domin shawo kan barkewar cutar.”
Ibrahim Muhammad ya bukaci Gwamna Yusuf da Kwamishinan Lafiya na jihar su samar da karin tallafin gaggawa ga al’ummomin da cutar ta shafa.
An shiga dimuwa kan mashako a Kano
Ibrahim Muhammad ya kuma bayyana damuwarsa kan sake barkewar cutar bayan irin wannan lamari ya faru a yankin a shekarar da ta gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Source: Facebook
A kalamansa:
“Mun bukaci Gwamna da Kwamishinan Lafiya su sake tura karin agajin gaggawa zuwa yankin saboda cutar ta yadu sosai a wannan wuri."
Da yake goyon bayan kudirin, dan majalisar da ke wakiltar mazabar Kiru, Usman Abubakar Tasi’u, ya ce cutar ta wuce Rano zuwa wasu al’ummomi a Kiru, ciki har da Kwarin Dangora, garin Dangora da Yelwa.
Usman Abubakar Tasi’u ya bayyana cewa wani shugaban matasan jam’iyyar APC a garin Kiru ya rasa ‘ya’ya biyu sakamakon cutar a rana guda.
Ya bukaci a kafa wani kwamitin gaggawa domin tunkarar cutar a kananan hukumomin da abin ya shafa, ciki har da Rano, Tudun Wada, Kibiya, Bunkure, Bebeji da Kiru.
Shi ma dan majalisar da ke wakiltar Dawakin Tofa, Saleh Ahmad, ya bukaci gwamnati ta kara kaimi wajen gudanar da allurar rigakafi da sauran matakan kariya.
Mutuwa ta girgiza APC a jihar Kano
A wani labarin, mun wallafa cewa Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya tabbatar da rasuwar sanannen dan siyasa a jihar Kano, Alhaji Hamza Darma.
Sanata Barau I Jibrin ya bayyana jimami bisa wannan rashi, yana mai cewa rasuwar Darma babban rashi ne ga daukacin al'ummar Kano ba jam'iyyar APC kawai ba.
Rahotanni sun nuna cewa manyan jiga-jigai ciki har da mataimakin gwamnan Kano, Murtala Sule Garo sun halarci jana'izarsa yayin da ake ci gaba da tura sakon jimami.
Asali: Legit.ng

