Kalaman Sanata Yari Sun Fusata ADC, Ta Yi Zazzafan Martani game da Mulkin APC
- ADC ta ce hasashen Abdul’Aziz Yari na cewa Bola Tinubu zai sake lashe zaɓen 2027 da APC za ta ci gaba da mulki bayan 2031 mafarki ne kawai
- David Mark ya ce APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba su da wani katabus da za su nuna wa jama'a har ta kai ga an zuba masu kuri'a a 2027
- Kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya tunatar da APC cewa PDP ma ta taɓa ikirarin za ta yi mulkin Najeriya na tsawon shekaru 80, abin ya zama tarihi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam’iyyar ADC ta mayar wa Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu, Sanata Abdul’Aziz Yari, martani.
Yari ya yi maganar cewa shugaba Bola Tinubu zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027, yayin da jam’iyyar APC mai mulki za ta ci gaba da riƙe mulki har bayan 2031.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa Shugaban ADC na ƙasa, Sanata David Mark, ya bayyana hasashen Yari a matsayin mafarki kawai, yana mai cewa kalaman sun yi hannun riga da hakikanin yanayin siyasar Najeriya.
Martanin ADC ga Sanata Yari
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Yari, tsohon gwamnan Jihar Zamfara, ya bayyana a ranar Lahadi 23 ga watan Agusta, 2026 cewa yana da yakinin Shugaba Tinubu zai sake lashe zaɓen 2027.
Sai dai da yake mayar da martani kan kalaman, David Mark ya ce Yari da jam’iyyarsa ta APC ba za su iya hasashen samun nasara ba, saboda ba su da wani saƙo da za su gabatar wa masu zaɓen Najeriya.
Da yake karin bayani ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Kola Ologbondiyan, shugaban ADC na ƙasa ya ce:
“Abin da Sanata Yari ya faɗa tunani ne na fata wanda ya yi hannun riga da hakikanin abin da ke faruwa a ƙasarmu."

Kara karanta wannan
Kurunkus: Danjuma Goje ya raba gardama kan batun ficewa daga APC zuwa wata jam'iyya
“Da farko dai, jam’iyyarsa ta APC da shugabanta, Bola Ahmed Tinubu, ba su da wani saƙo da za su gabatar wa masu zaɓen Najeriya. Ta yaya zai yi hasashen samun nasara a zaɓen da ba za su iya sadar da saƙonsu ga jama’a ba?”
Kakakin ADC ya yi kaca-kaca da kalaman Yari
A nasa bangaren, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na ADC, Bolaji Abdullahi, ya yi watsi da kwarin gwiwar Sanata Abdul’Aziz Yari na cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Source: Facebook
Abdullahi ya ce mutanen da ke tabbatar wa Tinubu cewa zai samu nasara cikin sauƙi a 2027 ba sa ba shi sahihin bayani game da halin siyasar ƙasar.
Ya ce:
“Yana daga cikin mutanen da ke yi wa Shugaba Tinubu ƙarya. Mun fahimci cewa yana buƙatar tabbatar da cancantar sabon muƙaminsa."
Kakakin ADC ya kuma tuna cewa a lokacin da jam’iyyar PDP ke mulki, ta taɓa ikirarin cewa za ta yi mulkin Najeriya na tsawon shekaru 80, amma daga baya aka kayar da ita a zaɓe.
Rikicin ADC ya kara kamari
A baya, kun ji cewa Shugaban tsagin ADC, Nafiu Bala, ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar kwanaki bayan ya yi maganar dawo da tallafin man fetur.
Nafiu Bala ya kuma yi zargin cewa Atiku da David Mark ba su da hurumin ikirarin cewa su ne shugabannin ko masu takarar shugaban kasa a jam'iyyar hadakar adawa ta ADC.
Ya bayyana cewa tsagin nasa ya gabatar da Chris Uba a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, yana mai cewa kotu ce za ta yanke hukunci kan takarar Atiku Abubakar.
Asali: Legit.ng

