'Kotu za Ta Hana Atiku Takarar 2027,' Nafiu Bala bayan Batun Tallafin Mai
- Shugaban tsagin ADC, Nafiu Bala, ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar kwanaki bayan ya yi maganar dawo da tallafin man fetur
- Nafiu ya kuma yi zargin cewa Atiku da David Mark ba su da hurumin ikirarin cewa su ne shugabannin ko masu takarar shugaban kasa a ADC
- Ya bayyana cewa tsagin nasa ya gabatar da Chris Uba a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, yana mai cewa kotu ce za ta yanke hukunci kan takarar Atiku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban tsagin ADC, Nafiu Bala, ya fito ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da wasu shugabannin jam’iyyar kan ikirarin cewa shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.
Maganar Atiku kan dawo da tallafin man fetur ta jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya, inda ta sanya wasu manyan ’yan siyasa, ciki har da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yin martani kan batun.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Source: Twitter
A wata hira da DCL Hausa a Facebook, Nafiu Bala ya bayyana cewa tsagin da yake jagoranta na ci gaba da tallata ’yan takararsa, yana mai gargadin Atiku Abubakar da David Mark.
Ya ce har gobe su ne shugabannin ADC, yana mai kira ga ’yan Najeriya da su yi watsi da ikirarin cewa Atiku Abubakar ne ɗan takarar shugaban ƙasa da jam’iyyar ta tsayar.
Nafiu Bala ya soki takarar Atiku
Nafiu Bala ya bayyana cewa ya yi mamakin yadda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta karɓi takarar Atiku Abubakar.
Ya ce tsagin nasu ya zauna da masu ruwa da tsaki na ADC, inda suka yanke shawarar miƙa takarar shugaban ƙasa zuwa Kudu tare da tsayar da Chris Uba a matsayin ɗan takararsu.
A cewarsa, Atiku Abubakar ba zai shiga zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a ƙarƙashin ADC ba, domin suna jiran hukuncin kotu da zai tabbatar da rusa takararsa.

Kara karanta wannan
Abin ya fara yi wa Tinubu yawa, jigon APC ya ba Atiku gaskiya kan dawo da tallafin fetur a Najeriya
Ya ce duk da cewa an saka sunan Atiku a shafin INEC a matsayin wanda zai yi takara, hakan ba ya nufin tsagin nasu ya amince da shi.
Maganar adawa da ADC
Nafiu Bala ya bayyana cewa ba ya adawa da jam’iyyar ADC, yana mai cewa ya shafe shekaru yana aikin gina jam’iyyar.
Ya ce yana jan kunnen Atiku Abubakar da dukkan ’yan takarar ADC da su kiyaye abin da yake kira da ƙoƙarin lalata tsarin jam’iyyar.

Source: Facebook
Ya kuma bukaci hukumomin duniya da su sanya Atiku Abubakar ido, yana zarginsa da kasancewa “makiyin dimokuraɗiyya”.
A hirar da aka yi da shi, Nafiu ya ce tsagin nasa ba zai yarda da abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarin karɓe ikon jam’iyyar ba.
Gargadi kan dawo da tallafin mai
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa yunkurin dawo da tallafin man fetur zai iya mayar da Najeriya baya ta fuskar tattalin arziki.
Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya ce dawo da tallafin zai iya rage kwarin gwiwar masu zuba jari tare da ƙara matsin lamba kan kuɗin gwamnati.
Ya ce dawo da tallafin zai iya mayar da Najeriya cikin yanayin tattalin arzikin shekarar 2022, tare da dawo da matsalolin ƙarancin man fetur.
Asali: Legit.ng