Da Gaske APC Ta Soke Kwamitin Kamfen Tinubu na 2027 bayan Maganganu?

Da Gaske APC Ta Soke Kwamitin Kamfen Tinubu na 2027 bayan Maganganu?

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi magana kan rahotannin da ke cewa ta janye jerin sunayen Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen
  • Sakataren Yaɗa Labarai na APC, Felix Morka, ya ce idan aka samu wani sauyi a jerin sunayen, jam’iyyar za ta sanar da shi yadda ya dace
  • Jam’iyyar ta fitar da jerin sunayen ranar Asabar, inda Bola Tinubu da Kashim Shettima suka zama shugabanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi martani game da rahotannin da ke cewa ta soke kwamitin yakin neman zabe.

Jam'iyyar ta musanta sauya jerin sunayen Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na 2027.

APC ta musanta labarin soke kwamitin yakin neman zabenta
Shugaba Bola Tinubu da shugaban APC a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

APC ta musanta soke kwamitin kamfen Tinubu

Felix Morka, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na APC, ya bayyana rahotannin a matsayin jita-jita yayin da yake magana da TheCable ranar Talata da safe.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Danjuma Goje ya raba gardama kan batun ficewa daga APC zuwa wata jam'iyya

Morka ya ce duk wani sauyi da za a yi wa jerin sunayen zai kasance a hukumance kuma za a sanar da jama’a yadda ya dace.

Ya ce:

“Jita-jita ba labari ba ce. Idan mutane suna yaɗa jita-jita, wannan ba labari ba ne. Akwai labaran ƙarya, sannan akwai sahihan labarai.
"A yanzu babu wanda zai bayar da wani jerin suna. Amma idan akwai wani dalilin sabunta shi, za a sanar da hakan yadda ya dace.”
APC ta fitar da kwamitin yakin neman zaben Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Yadda aka kafa kwamitin yakin neman zabe

A ranar Asabar, APC ta bayyana jerin sunayen Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na 2027, inda aka naɗa Shugaba Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a matsayin shugaba da mataimakinsa.

An kuma naɗa Nentawe Yilwatda, Shugaban APC na Ƙasa, a matsayin mataimakin shugaban kwamitin, cewar Punch.

An naɗa Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan Zamfara, a matsayin Darakta-Janar, yayin da Hope Uzodimma, Gwamnan Imo kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Progressive, aka naɗa sakataren kwamitin.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Haka kuma, Betta Edu, tsohuwar Ministar Harkokin Jinƙai da Rage Talauci; Ngozi Olejeme, tsohuwar shugabar hukumar Nigeria Social Insurance Trust Fund; Zacch Adedeji, Shugaban Hukumar Haraji ta Najeriya, da Taminu Yakubu, Darakta-Janar na Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya, na cikin mambobin kwamitin.

Sai dai kafa kwamitin ya jawo ce-ce-ku-ce, musamman saboda shigar wasu jami’an gwamnati masu ci da kuma mutanen da ake zargi da hannu cikin badakalar kuɗi.

A ranar Litinin ne rahotanni suka fara yaduwa cewa jam'iyyar APC ta janye jerin sunayen domin sake duba wasu daga cikin mutanen da aka saka.

Da aka tambayi Morka kan korafe-korafen wasu ’yan jam’iyyar game da rashin saka wasu fitattun ’yan APC a cikin jerin, ya ce ba shi ne mutumin da ya dace ya yi magana kan wannan batu ba.

Nentawe ya magantu kan dawo da tallafin mai

An ji cewa shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda ya ce bai dace a mayar da manufofin tattalin arziki zuwa alkawuran lokacin zaɓe ba.

Nentawe ya kuma maida martani ga dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar kan kudirinsa na dawo da tallafin mai.

Shugaban APC ya buƙaci Atiku ya bayyana inda kuɗin da zai yi amfani da su wajen dawo da tallafin fetur za su fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.