Batun Dawo da Tallafin Mai Ya Tada Hankalin Shugaban APC na Kasa, Ya Tura Tambaya 1 ga Atiku

Batun Dawo da Tallafin Mai Ya Tada Hankalin Shugaban APC na Kasa, Ya Tura Tambaya 1 ga Atiku

  • Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda ya ce bai dace a mayar da manufofin tattalin arziki zuwa alkawuran lokacin zaɓe ba
  • Nentawe ya kuma maida martani ga dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar kan kudirinsa na dawo da tallafin mai
  • Shugaban APC ya buƙaci Atiku ya bayyana inda kuɗin da zai yi amfani da su wajen dawo da tallafin fetur za su fito

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya soki shirin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar na dawo da tallafin man fetur.

Yilwatda ya bayyana shirin a matsayin sauyin matsaya mai matuƙar tayar da hankali, yana mai cewa bai kamata batun dawo da tallafi ya zama abin da za a yi alkawari kawai a lokacin zaɓe ba.

Kara karanta wannan

'Kotu za ta hana Atiku takarar 2027,' Nafiu Bala bayan batun tallafin mai

Nentawe.
Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentae Yilwatda a ofishin jam'iyya da ke birnin Abuja Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Punch ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Abimbola Tooki, ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Shugaban APC ya ce ’yan Najeriya sun cancanci a yi musu cikakken bayani kan duk wani shirin dawo da tallafin da zai sake jefa gwamnati cikin babban nauyin kuɗi.

Me APC ta ce game da tallafin?

Yilwatda ya yi wannan magana ne yayin ziyarar da ya kai hedikwatar City Boy Movement da ke Abuja, inda ya duba wuraren gudanar da ayyukan ƙungiyar tare da tattaunawa da shugabanninta.

Ya ce an shafe shekaru uku ana ƙalubalantar ’yan adawa da su bayyana wa ’yan Najeriya abin da za su yi dabam idan aka ba su ikon mulki, amma babu wani cikakken shiri mai ma’ana da gamsarwa da suka gabatar.

A cewarsa, abin tambaya ne yadda Atiku, bayan sama da shekaru uku ba tare da gabatar da tsarin mulki ba, ya fito da shirin da zai iya sauya wasu gyare-gyaren tattalin arziki da aka yi.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Tambayar da APC ta tura wa Atiku?

Farfesa Yilwatda ya ce shirin dawo da tallafin fetur na iya mayar da tsarin ci gaban ƙasar baya da shekaru.

Ya ce:

“Manufofin tattalin arziki ba za a mayar da su alkawuran lokacin zaɓe ba. ’Yan Najeriya sun cancanci sanin ainihin inda kuɗin da za a dawo da tallafin zai fito.
“Waɗanne ɓangarori ne za su ɗauki nauyin hakan, kuma ko za a iya dorewar irin wannan manufa ba tare da sake buɗe matsin kuɗin da ya sa aka yi gyaran tattalin arzikin ba?”

Me ya sa Yilwatda ya kare cire tallafi?

Shugaban APC ya ce ainihin jarabawar shugabanci ba ita ce iya yin alkawarin agaji cikin gaggawa domin samun ƙuri’a ba, illa jajircewa wajen ɗaukar matakai masu wahala da kuma bayyana dalilansu ga jama’a.

Ya ce gwamnati na buƙatar ci gaba da aiwatar da manufofin da za su samar da ci gaba mai ɗorewa, maimakon komawa ga tsare-tsaren da za su iya sake jefa tattalin arzikin cikin matsin kuɗi.

Kara karanta wannan

Bayan abubuwa sun ɗauki zafi, an fito da gaskiyar shirin Atiku na dawo da tallafin mai a Najeriya

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a wurin taron kaddamar da hadaka a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Yilwatda ya ce ’yan Najeriya sun isa su fahimci bambanci tsakanin manufofin da ke magance matsalolin tattalin arziki na asali da alkawuran da za su iya kawo sauƙi na ɗan lokaci amma su haifar da ƙarin matsala a nan gaba.

Jigon APC ua goyo bayan dawo da tallafi

A wani rahoton, kun ji cewa wani jigon APC a jihar Neja, Jonathan Vatsa, ya goyi bayan sukar da Atiku Abubakar ya yi kan cire tallafin man fetur.

Ya ce manufar cire tallafin ta jefa ’yan Najeriya cikin tsananin wahala ba tare da samar musu da wata fa’idaBmai ma’ana ba, yana mai kira ga Tinubu ya canza tunani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262