Jigo a APC kuma Dan Kasuwar Mai Ya Kwancewa Atiku Zani kan Dawo da Tallafin Fetur

Jigo a APC kuma Dan Kasuwar Mai Ya Kwancewa Atiku Zani kan Dawo da Tallafin Fetur

  • Jigon APC a Kebbi, Aminullah Mustapha, ya yi Allah-wadai da alkawarin Atiku Abubakar na mayar da tallafin mai idan ya zama shugaban kasa
  • Aminullah Mustapha ya ce tsarin tallafin mai ya yi fama da karkatar da kudaden gwamnati da almundahana
  • Ya ce cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi ya kasance matakin da ya dace domin magance matsalolin tsarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma dan kasuwar man fetur a Jihar Kebbi, Aminullah Mustapha, ya yi wa Atiku Abubakar martani kan batun dawo da tallafin fetur.

Aminullah Mustapha yi Allah-wadai da sanarwar da Atiku Abubakar ya yi na cewa zai mayar da tallafin mai idan aka zabe shi shugaban kasa.

Atiku na shan suka kan batun dawo da tallafi
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta ce ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Lahadi, 23 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya kuncowa Tinubu kura kan batun maido tallafin man fetur

Mustapha ya bayyana wannan kudiri a matsayin yunkurin dawo da wani tsari da ya ce ya kasance cike da cin hanci da rashawa da kuma cin zarafin tsarin, yana mai cewa komawa tsarin tallafin mai ba zai amfani ’yan Najeriya ba.

Tsohon mai neman takarar kujerar Majalisar Wakilai a karkashin ADC, wanda ke da kwarewa a harkar man fetur, ya ce tsarin tallafin mai ya yi fama da karkatar da kudaden jama’a da kuma yin amfani da su ba bisa ka’ida ba.

Yadda ake karkatar da kudaden tallafi

Mustapha ya ce:

“A lokacin tsarin tallafin mai, kudade masu yawa da aka ware wa ’yan kasuwar man fetur ba su zuwa wuraren da aka tsara su je ba. Ana ware kudade ga wasu ’yan kasuwa na bogi domin su kai tankokin man fetur wani wuri, amma sai su karbi kudin ba tare da sun kai wani mai ba.”

Ya kara da zargin cewa wasu tankokin man fetur da aka biya kudinsu karkashin tsarin tallafin sun kare a kasashen makwabta kamar Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin, lamarin da ya bai wa wasu kasashe damar amfana da kudaden da aka ware domin tallafa wa man fetur ga ’yan Najeriya.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa Nyesom Wike bai zama darakta janar na kamfen Tinubu ba'

“Wasu tankokin man fetur da aka biya kudinsu karkashin tsarin tallafin mai sun kare a kasashen makwabta kamar Nijar da Benin. Wannan na nufin wasu kasashe suna cin gajiyar tallafin da aka tanada domin ’yan Najeriya,” in ji Mustapha.

'Yan kasuwa na yadda suke so

Ya kuma ce akwai zarge-zargen cewa an biya wasu masu mallakar wuraren ajiye man fetur kudaden shigo da kayayyakin man fetur, amma ba su shigo da kayayyakin cikin kasar nan ba.

“Akwai zarge-zargen cewa an biya wasu masu wuraren ajiye man fetur kudaden shigo da kayayyakin man fetur, amma ba su shigo da kayayyakin kasar nan ba. A wasu lokuta, ana zargin sun karbi kudin ne tun kafin kayayyakin da aka shigo da su su iso Najeriya,” in ji shi.

Mustapha ya kare Tinubu

Jigon APC din ya ce Shugaba Bola Tinubu ya nuna jarumtaka wajen cire tallafin man fetur, yana mai cewa matakin ya zama dole domin magance abin da ya kira cin hanci da rashawa da rashin inganci da suka dade suna addabar tsarin.

“Shugaba Tinubu ya nuna jarumtaka kuma ya kasance mai gaskiya ga ’yan Najeriya ta hanyar cire tallafin. Shugabannin Najeriya da dama, ciki har da Atiku Abubakar, sun san cewa tsarin tallafin ya yi fama da cin hanci da rashawa, amma saboda tsananin son siyasa, ba sa son su gaya wa ’yan Najeriya gaskiya,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Kalubalen da ke gaban Atiku kan maganar dawo da tallafin mai idan ya yi nasara

Atiku na ci gaba da shan suka kan dawo da tallafin fetur
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: @atiku
Source: Twitter

Hadimin Atiku ya soki cire tallafin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai magana da yawun Atiku Abubakar, Kenneth Okonkwo, ya soki matakin gwamnatin tarayya na cire tallafin man fetur.

Kenneth Okonkwo ya ce cire tallafin bai kawo sauƙin rayuwa ga 'yan Najeriya ba, sai ma kara jefa su cikin matsananciyar wahala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng