Bayan Abubuwa Sun Dauki Zafi, An Fito da Gaskiyar Shirin Atiku na Dawo da Tallafin Mai a Najeriya

Bayan Abubuwa Sun Dauki Zafi, An Fito da Gaskiyar Shirin Atiku na Dawo da Tallafin Mai a Najeriya

  • Kenneth Okonkwo, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar ya yi karin haske kan batun dawo da tallafin mai
  • Ya ce shirin dawo da tallafin man fetur ba zai koma tsarin tallafin da ake zargin ya cika da matsaloli a baya ba
  • Okonkwo ya ce shirin Atiku zai mayar da hankali ne kan samar da man fetur mai sauƙin farashi ga talakawa ta hanyar matatun mai na cikin gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kenneth Okonkwo, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kare sukar da ake yi wa shirin dawo da tallafin fetur.

Okonkwo ya ce manufar shirin ita ce rage farashin man fetur ga talakawan Najeriya, yana mai cewa ba shi da alaƙa da tsohon tsarin tallafin man fetur da aka yi amfani da shi a baya.

Kara karanta wannan

Atiku ya ɗauki zafi, ya sake fallasa abin da yan Najeriya ba su sani ba kan tallafin man fetur

Kenneth Okonkwo.
Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Kenneth Okonkwo Hoto: Kenneth Okonkwo
Source: Twitter

Okonkwo ya kare shirin Atiku

Ya yi wannan bayani ne yayin da yake magana a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels TV.

Okonkwo ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kuskuren fahimtar manufar Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC a zaben 2027.

Atiku ya bayyana a ranar Laraba cewa zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027, lamarin da ya haifar da cece-kuce musamman saboda matsayin da ya taɓa ɗauka kan cire tallafin a lokacin kamfen 2023.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da rashin bayyana yadda aka yi amfani da kuɗaɗen da aka tara sakamakon cire tallafin man fetur.

Atiku na shirin dawo da tsarin baya?

Tinubu ya mayar da cewa hakan alama ce ta “tsananin jahilci game da mulki da tattalin arziki”, tare da jaddada cewa tsarin tallafin man fetur ya jefa ƙasar cikin matsala mai girma.

Kara karanta wannan

Jigo a APC kuma dan kasuwar mai ya kwancewa Atiku zani kan dawo da tallafin fetur

Sai dai Okonkwo ya ce Atiku ba ya shirin komawa tsohon tsarin tallafin man fetur, wanda ya dogara da shigo da man fetur daga ƙasashen waje da kuma zargin almundahana wajen biyan tallafin.

“Babbar manufar shirin Atiku ita ce samar da man fetur mai sauƙin samu da araha ga talakan Najeriya. Jahilcin Tinubu ne ya sa yake cewa Atiku yana son komawa tsohon tsarin tallafi," in ji shi.
Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Abin da tsarin Atiku ya kunsa

A cewar Okonkwo, shirin da Atiku ya kira Atiku Fuel Affordability Plan (AFAP) ya dogara ne kan samun isasshen ƙarfin tace danyen mai a cikin gida da taimakon gwamnati wajen tabbatar da matatu sun samu kaya kan farashi mai sauƙi.

Ya ce samar da danyen mai ga matatun cikin gida kan farashin da ya dace zai rage kuɗin samar da man fetur, wanda hakan zai ba da damar sayar da shi ga ’yan Najeriya cikin sauƙi.

A cewarsa, da a ce gwamnatocin baya sun tabbatar da samun isasshen ƙarfin tace man fetur a cikin gida da wadataccen mai, da ba a samu buƙatar tallafin man fetur tun farko ba, kamar yadda Vanguard ta kawo.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya kwantowa Tinubu kura kan batun maido tallafin man fetur

Atiku ya dge kam dawo da tallafi

A wani labarin, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na ADC Atiku Sbubakar ya ce babu abin da zai hana shi dawo da tallafin mai da ya yi wa ’yan Najeriya alkawari.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ikirarin Tinubu na cewa ya cire tallafin mai yaudara ce kawai, domin yana biyan tallafi amma da sunan rangwamen haraji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262