Amaechi: Mataimakin Atiku Ya Bukaci 'Yan Najeriya Kada Su Zabi ADC, an Ji Dalili

Amaechi: Mataimakin Atiku Ya Bukaci 'Yan Najeriya Kada Su Zabi ADC, an Ji Dalili

  • Rotimi Amaechi ya bukaci ’yan Najeriya su zabi ’yan takara bisa kwarewa da tarihin ayyukansu a zaben 2027
  • Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce kada a zabi jam’iyyar ADC da yake takara a karkashinta, inda ya kawo dalilinsa
  • Amaechi ya ce rashin jituwa kan wanda zai zama dan takarar shugaban kasa ya kawo cikas ga hadin kan jam’iyyun adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers - Rotimi Amaechi, dan takarar mataimakin shugaban kasa na African Democratic Congress (ADC), ya bukaci ’yan Najeriya su zabi ’yan takara bisa kwarewa a zaben 2027.

Rotimi Amaechi ya bayyana cewa kada 'yan Najeriya su zabi jam’iyyar ADC idan ba za ta iya yin abin da ya dace ba.

Amaechi ya ba 'yan Najeriya shawara
Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi Hoto: @ChibuikeAmaechi
Source: Twitter

Amaechi ya bayyana hakan ne yayin wani zama na kwamitin tattaunawa a taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) na 2026 da ake gudanarwa a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers ranar Litinin, 24 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Danjuma Goje ya raba gardama kan batun ficewa daga APC zuwa wata jam'iyya

Amaechi ya sanar da mahalarta taron cewa:

“ADC tana samar da wani sabon salo na shugabanci gaba daya. Idan ba za mu iya yin abin da ya dace ba, kada ku zabe mu." In ji shi.

An so 'yan hadawa su hade waje guda

Jawabin Amaechi ya zo ne watanni kadan kafin babban zaben 2027, yayin da ake ci gaba da kira ga jam’iyyun adawa su hada kai domin kwace mulki daga hannun jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A bara, jam’iyyun adawa sun gudanar da wani taro a Ibadan, jihar Oyo, inda suka amince da tsayar da dan takara guda a zaben shugaban kasa.

Sai dai har yanzu jam’iyyun adawar ba su cimma matsaya kan wanda zai zama dan takararsu a zaben shekara mai zuwa ba.

Amaechi ya bayyana matsalar hadaka

A taron NBA, Amaechi ya ce rashin iya cimma matsaya tsakanin ’yan takara ya sanya hadin kan jam’iyyun adawa ya zama mai wahala.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

“Hadaka kamar yadda take a yau, yana da wahala a cimma ta. Idan hakan zai yiwu, na tabbata Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar zai kasance a shirye ya shiga cikinta."
“Amma matsalar ita ce kowa yana da burinsa; babu wanda yake son ya hakura. Akwai ’yan siyasa kalilan da suke kaunar Najeriya. Abin da ’yan siyasa suke yi shi ne kawai su shigo su kwashe albarkatun kasar,” in ji shi.

Ya kare tarihin mulkinsa

Sai dai tsohon ministan ya kare tarihin ayyukansa a mukaman gwamnati, yana mai cewa har yanzu ana iya ganin ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar a jihar Rivers.

Amaechi, wanda ya wakilci dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci ’yan Najeriya su yi watsi da bambancin kabila wajen zaben shugabanni, su kuma duba tarihin ayyukan ’yan takara.

“Hadaka ya kamata ta kasance bisa kwarewa da aiki,” in ji shi.

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na ADC ya kara da cewa:

“Ku tantance mu bisa ayyukan da muka yi a baya sannan ku zaba; kada ku zabe mu kawai saboda kai dan Ikwerre ne ko Omoku, sannan ka zabi dan takararka.”

Kara karanta wannan

"Ba sabon alkawari ba"; Abin da Gwamna Radda zai yi kamfen da shi a Katsina

Amaechi ya fadi abin da Najeriya ke so

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana shirin da yake da shi ga Najeriya idan ya zama shugaban kasa.

Amaechi ya bayyana cewa Najeriya tana buƙatar sabuwar hanyar siyasa wadda ta ginu a kan rage talauci, samar da ayyukan yi, riƙon amana, da kuma bin doka da oda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng