
Jihar Ebonyi







Gwamnan Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya dawo da kwamishinoni guda uku da aka dakatar, ciki har da na Kananan Hukumomi, Lafiya, da Albarkatun Ruwa.

An yi ta ce-ce-ku-ce bayan gwamnatin jihar Ebonyi ta bukaci shugabannin kananan hukumomi 13 su dauki nauyin akalla Mahajjaci daya don aikin Hajjin 2025.

Hatsarin mota ya kashe matashiya mai shirin yiwa kasa hidima a hanyar Afikpo, Ebonyi. Sauran matasa sun ji rauni kuma an garzaya da su asibitin DUFUHS.

Jam'iyyar PDP reshen jihar Ebonyi ta zaɓi Chidiebere Egwu a matsayin wanda zai maye gurbin mataimakin shugabanta na dhiyyar Kudu maso Gabas, Ali Odefa.

Rundunar ‘yan sanda ta kama mutane 17 a Afikpo, Ebonyi, bayan sun kashe Uromchi Okorocha bisa zargin maita. Sufeto Janar ya la’anci daukar doka a hannu.

Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya halarci wurin taron rabon kayan tallafi na wani ɗan majalisar tarayya na LP, ya ce babu gaba ko ƙiyayya a siyasa.

Gwamnaan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya ba shugabannin kananan hukumomi wa'adi domin su biya ma'aikatan da ke karkashinsu hakkokin da suke bin bashi.

Ma'aikatan Ebonyi za su dara. Gwamnansu, Francis Nwifuru zai gwangwajesu. Za a ba kowane ma'aikaci kyautar N150,000 don shagalin bikin kirismimeti.

Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya ce mahaifinsa na fuskanci tsana, hassada da tsangwama a kauyensu sabida Allah ya masa arziki lokaci guda.
Jihar Ebonyi
Samu kari