Gwamna David Umahi ya fada ma mutanen jihar Ebonyi wanda za su zaba tsakanin Tinubu da Peter Obi

Gwamna David Umahi ya fada ma mutanen jihar Ebonyi wanda za su zaba tsakanin Tinubu da Peter Obi

  • Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya umurci al'ummar jihar da kada su zabi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi
  • Umahi ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu za su yi a jiharsa
  • Sai dai kuma, gwamnan ya nuna takaicinsa kan yadda shugabanni da deliget din yankinsu na kudu maso gabas suka sayar da kuri'unsu a zaben fidda gwanin APC

Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya bukaci al’ummar jiharsa da su karbi katinsu na zabe sannan su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu.

Gwamna Umahi ya bukaci mazauna jihar da kada su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, Channels Tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya saki jerin sunayen jiga-jigan APC da wasu mutane da basa son Bola Tinubu

Ya kuma shawarce su da su karbi katin zabensu kafin a rufe shirin a ranar 29 ga watan Yunin 2022.

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi
Gwamna David Umahi ya fada ma mutanen jihar Ebonyi wanda za su zaba tsakanin Tinubu da Peter Obi Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Umahi ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Jam’iyyarmu ita ce APC ba Labour Party ba. Ba za mu zabi Labour Party ba. APC za mu zaba.
“Jihohin da Labour Party ta taimaka su zabe su.
“Ajandar Ubangiji kan jihar Ebonyi shine ajandar jihar Ebonyi kuma wannan shine abun da ya kamata ku dunga gaya masu idan suka zo tambayarku wa za ku zaba. Ku fada masu kada su nemi kuri’unmu, kuri’unmu na APC ne.”

Gwamnan ya bayar da umurnin ne a ranar Litinin, 13 ga watan Yuni yayin rantsar da sabbin jami’an jihar zauren gwamnati da ke Abakaliki, jaridar The Cable ta rahoto.

Ya koka da karancin rijista a jihar baya ga kananan hukumomin Afikpo ta Kudu da Onicha da ke da sabbin masu zabe da aka yiwa rijista guda 71,000 da 32,000.

Kara karanta wannan

2023: Watakila Bola Tinubu ya dauki Musulmi a ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa

“Abin takaici ne yadda har yanzu ba a samu mutane sun fita yin rijista ba a kananan hukumomi daban-daban na jihar, baya ga yankin Afikpo ta kudu da ta samu mutane 71,000 da suka yi rijista, har yanzu sauran ba su tabuka komai ba.”

Umahi ya caccaki shugabanni da deliget daga yankin Kudu maso Gabas bisa zargin sayar da kuri’unsu ga ’yan takarar da suka fito daga wasu yankunan a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC da aka kammala.

Umahi ya ce “abun kunya ne.”

Gwamnan ya ce ya yi kuka sosai da ganin sakamakon zaben fidda gwanin jam’iyyar, inda ya ce akwai zafi ‘yan kabilar Igbo su rika ihun cewa an mayar da su saniyar ware, kuma duk lokacin da suka samu damar tabuka wani abu sai su sayar da kuri’unsu.

Kwankwaso ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2023, in ji wani malamin addini

Kara karanta wannan

Bayan rasa tikitin gaje Buhari, gwamna ya karbe tikitin sanata na APC a hannun kaninsa

A wani labarin, shugaban kungiyar kare hakkin Kirista da Musulmi, Prophet Iwu Jideogu Ogbu, ya bayyana wanda zai lashe babban zaben 2023 mai zuwa.

A cewar Ogbu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ne zai lashe babban zaben mai zuwa.

Kwankwaso ne zai daga tutar jam’iyyar NNPP wacce ta shafe shekaru sama da 20 amma ba’a jinta bayan ya farfado da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel