Tsohon Gwamnan Ebonyi, David Umahi, Zai Yi Murabus Daga Kujerar Sanata

Tsohon Gwamnan Ebonyi, David Umahi, Zai Yi Murabus Daga Kujerar Sanata

  • Mataimakin jagoran majalisar dattawa, Sanata Dave Umahi, ya fara shirye-shiryen aje muƙaminsa a majalisar tarayya
  • Sanata Umahi na shirin murabus daga kujerar Sanata baya naɗin da shugaba Bola Tinubu ya masa a cikin ministoci
  • Jigon jam'iyyar APC ya riƙe kujerar gwamna da mataimakin gwamna a jihar Ebonyi da ke shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - David Umahi, mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa ta 10, ya fara shirye-shiryen sauka daga muƙaminsa na Sanata, jaridar Bussinesday ta rahoto.

Sanata Umahi tare da shugaba Tinubu.
Tsohon Gwamnan Ebonyi, David Umahi, Zai Yi Murabus Daga Kujerar Sanata Hoto: Barr Chioma Nweze
Asali: Facebook

Meyasa tsohon gwamnan zai hakura da kujerar Sanata?

Umahi, tsohon gwamnan jihar Ebonyi ya fara yunkurin sauka daga matsayin sanata ne sakamakon naɗin da aka masa na Minista karkashin mulkin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon gwamnan, wanda ke wakiltar mazaɓar Sanatan Ebonyi ta kudu a majalisar tarayya ta 10, yana daga cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Jerin Asalin Jihohin Ministoci 28 Da Shugaba Bola Tinubu Ya Naɗa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Umahi da wasu kusoshin siyasar ƙasar nan sun shiga cikin ministoci

Yana cikin manyan jiga-jigan siyasa da shugaba Tinubu ya zaƙulo ya naɗa a a matsayin ministocinsa, waɗanda tuni sunayensu suka isa majalisar dattawa.

Daga cikin waɗan nan jiga-jigan har da abokin Umahi kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike, da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, Leadership ta rahoto.

A ɗazu shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya tabbatar da zuwan sunayen kuma ya karanto su ɗaya bayan ɗaya a a zauran majalisa ranar Alhamis.

Ya kuma bayyana cewa nan ba da jima wa ba shugaban kasa zai sake turo ƙarin sunayen waɗanda ya naɗa ministoci domin tantancewa.

Tun da jima wa 'yan Najeriya suka ƙosa su ji sunayen ministocin shugabam ƙasa domin sa ido su ga rawar da tawagar zata taka a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Mata 7 Daga Jihohin Katsina, Imo, Abia da Anambra da ke Shirin Zama Ministoci

Shugaba Tinubu: Jihohin Mutane 28 Da Shugaba Tinubu Ya Nada Ministoci Sun Bayyana

A wani rahoton na daban kuma mun tattara muku jerin sunayen asalin jihohin Ministoci 28 da shugaban ƙasa ya miƙa wa majalisar dattawan Najeriya.

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne ya kai sunayen ministocin yayin da Sanatoci ke tsaka da zamansu na yau Alhamis, 27 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel