Tsohon Dan Takarar APC a Kano Ya Fadi Dalilin Goyon Bayan Tinubu

Tsohon Dan Takarar APC a Kano Ya Fadi Dalilin Goyon Bayan Tinubu

  • Fahad Muhammad Dankabo da ya taba neman takarar kujerar majalisar wakilai a Kano, ya bayyana goyon bayansa ga tazarcen Tinubu
  • Dan siyasar ya zayyano abin da ya ja hankalinsa har ya karkata wajen goyon bayan mai girma Bola Tinubu ya ci gaba da mulkin Najeriya
  • Fahad Dankabo ya bayyana cewa shugaban kasar ya yi namijin kokari ta hanyar sakarwa kananan hukumomi mara kan kudadensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Fahad Muhammad Dankabo da ya kasance tsohon dan takarar kujerar majalisar wakilai ta Kabo da Gwarzo a jam’iyyar APC, ya yi magana kan goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu.

Hon Fahad Muhammad Dankabo ya fito ya bayyana dalilin da ya sa yake goyon bayan sake zaben mai girma Bola Tinubu a babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Kara karanta wannan

Maganganun da Tinubu ya gayawa Gwamna Adeleke bayan sun kebe a Aso Villa

Fahad Dankabo na goyon bayan tazarcen Tinubu
Fahad Muhammad Dankabo da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Fahad Muhammad Dankabo, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Dan siyasar ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 23 ga watan Agustan 2026.

Meyasa Dankabo ya ke goyon bayan tazarcen Tinubu?

Fahad Muhammad Dankabo ya bayyana cewa yana goyon bayan Shugaba Tinubu ne musamman kan matakin bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu ta fuskar kudaden shiga da gudanar da kasafin kudi, matakin da ya ce ya samu goyon bayan Kotun Koli.

A cewarsa, wannan mataki na da matukar muhimmanci saboda yana bai wa gwamnatocin kananan hukumomi damar mayar da hankali kai tsaye kan bukatun al’ummominsu, ciki har da ilimi, kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa da sauran ayyukan ci gaba.

Ya ce idan aka tabbatar da cewa kudade suna isa kai tsaye ga matakin gwamnati mafi kusa da jama’a, hakan zai taimaka wajen bunkasa ci gaba daga matakin kasa, tare da bai wa shugabannin kananan hukumomi da kansiloli damar samar da sakamako ga al’ummominsu.

Kara karanta wannan

Abin da Atiku zai yi don magance rashin tsaro cikin kwana 100 idan ya zama shugaban kasa

Dankabo ya yi kira ga 'yan Arewa

Dan siyasar ya kuma yi kira ga ‘yan Arewa da ke sukar gwamnatin Tinubu da su daina dora dukkan matsalolin da ke cikin al’ummominsu kacokan kan shugaban kasa.

“Shin da gaske komai laifinsa ne? Amsar ita ce a’a. Ya kamata mu kare manufofinsa domin ya ba wa shugabannin iko wato shugabannin kananan hukumominmu da kansiloli wadanda suka fi dacewa su samar da sakamako ga mutanenmu daga kasa." In ji shi.

Ya ce ya kamata jama’a su fara tambayar shugabannin kananan hukumominsu da kansilolinsu game da ayyukan da suke yi, musamman idan ana fuskantar matsaloli a fannin ilimi, kiwon lafiya, hanyoyi da sauran ababen more rayuwa.

A cewarsa, lokaci ya yi da jama’a za su fara bibiyar ayyukan shugabannin gwamnati a kowane mataki, maimakon dora dukkan alhakin gazawar kananan hukumomi kan Shugaban kasa.

Fahad Dankabo na goyon bayan Tinubu
Fahad Muhammad Dankabo na jawabi a wajen taro Hoto: Fahad Muhammad Dankabo
Source: Facebook

Dankabo ya kammala bayaninsa da yin kira ga jama’a da su yi wa kansu da shugabanninsu adalci, tare da rike kowane shugaba da alhakin da ya rataya a wuyansa.

Kara karanta wannan

"Na tausaya masa": Jigon PDP ya hango matsalar da za ta tunkari Tinubu idan ya yi tazarce

Kwankwaso ya ba Yari shawara kan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ba Sanata Abdulazi Yari shawara.

Madugun na Kwankwasiyya ya bukaci tsohon gwamnan na jihar Zamfara da ya sake tunani kan jagorantar kamfen din Shugaba Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng