Wata Sabuwa: Tun kafin Lokaci, An Kammala Tsara Wanda Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa a 2027
- Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya ce sauye-sauyen siyasa a ƙasar nan sun ƙara ƙarfafa goyon bayan Shugaba Bola Tinubu
- Wike ya yi ikirarin cewa duba da abubuwan da ke faruwa, an riga an kammala babban zaben shugaban kasa na 2027
- Wike ya yi watsi da batun akwai babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, yana mai cewa alami sun nuna Tinubu ne zai ci zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa an riga an kammala zaɓen 2027 kuma alamu sun nuna Shugaba Boka Tinubu ne mai nasara.
Wike ya kara da cewa sauye-sauyen siyasa da ake samu a faɗin ƙasar na nuna irin dumbin goyon baya da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ke kara samu.

Source: Facebook
Ministan Abuja ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai ranar Juma’a, 21 ga watan Agusta, 2026, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.
Wike ya ce an kammala zaben 2027
Ministan ya ce za a samu ƙarin sauye-sauyen siyasa da za su nuna goyon baya ga Shugaban Ƙasa a kwanaki masu zuwa, yana mai bayyana abubuwan da ke faruwa a matsayin wani ɓangare na babban sauyin tsarin siyasa.
“Nan da mako mai zuwa, ku kalli abin da zai faru. Za ku ga babban sauyin tsarin siyasa a wannan ƙasa, duk na na goyon bayan Mai Girma Shugaban Ƙasa."
“wannan dalili shi ne ya sa na ce an kammala wannan zaɓe. An kammala shi, don haka babu abin da wani zai iya yi,” in ji shi.
Wike ya caccaki Dele Momodu
Wike ya kuma caccaki tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Dele Momodu, kan yawan ambaton alaƙarsa da Ile-Ife, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Rasuwar babban jigon APC a Kano ta taɓa Shugaba Tinubu ana shirin fara kamfen 2027
“Ban san ina Dele Momodu yake ba, duk lokacin da kuka gan shi a talabijin, ya ce an haife shi a Ife. Ko dai ya ce an haife shi a Ife ne yana tunanin hakan zai sa Adeleke ya koma bangarensu.
Ministan Abuja ya ce wasu ’yan siyasa na iya bayyana a fili cewa suna goyon bayan PDP, amma a aikace suna kare APC, yana mai cewa hakan shaida ce ta samuwar babbar ƙawancen siyasa.
“Za ku ga mutum ya ce, ‘Ina goyon bayan PDP, ina goyon bayan PDP’, amma sai ya kare APC, kun ga wannan ai kawance ne,” in ji shi.
Wike ya ce zaɓen 2027 zai kasance mai ban sha’awa, yana mai cewa abubuwan da za su faru a sassa daban-daban na ƙasar za su bayyana waɗanda ke goyon bayan Shugaban Ƙasa.

Source: Twitter
Wike ya fadi burinsa kan Atiku da Obi
A wani rahoton, kun ji cewa ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya bayyana burinsa na kara wa Atiku Abubakar da yan adawa hawan jini a fagen siyasa kafin 2027.
Wike ya bayyana cewa ba aikinsa ba ne ya tabbatar da cewa ’yan adawa sun ji daɗin yanayin siyasar da ake ciki, domin burinsa shi ne ganin tawagarsa ta samu nasara.
Asali: Legit.ng
