Atiku Ya Haska Kokarinsu na Fito da El Rufai, Ya Fadi Abin da Ya Hana a Kama Shi

Atiku Ya Haska Kokarinsu na Fito da El Rufai, Ya Fadi Abin da Ya Hana a Kama Shi

  • Atiku Abubakar yana ganin ba daidai ba ne a zargi jagororin su na jam'iyyar ADC da watsi da Nasir El-Rufai
  • ‘Dan takaran shugaban kasar ya ce suna yin duk mai yiwuwa saboda tsohon gwamnan na Kaduna ya dawo gida
  • Atiku ya ce babu abin da ya hana shi a kama shi face bai aikata wani laifi ba lokacin da yake kan madafun iko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Atiku Abubakar ya sake tabo zancen tsare Nasir Ahmad El-Rufai da hukumomin Najeriya suke ci gaba da yi.

A wata hira da aka yi da shi, ‘dan takarar shugaban kasar na ADC a zaben 2027 ya ce ba su yi watsi da Nasir Ahmad El-Rufai.

Atiku El-Rufai
'Dan takaran shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar da tsohon gwamna Nasir El-Rufai Hoto: Atiku Abubakar/Nasir El-Rufai
Source: Facebook

An tuna wa Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai

A shafinsa na X, wani matashin ‘dan adawa a Najeriya, Emma Ukeh ya wallafa bangaren hirar da aka yi da Alhaji Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Malamin addini da ke goyon bayan Tinubu ya magantu kan tallafin mai

‘Yan jarida sun fada masa cewa wasu suna ganin ‘yan jam’iyyar ADC ba su yi abin da ya kamata domin a fito da El-Rufai ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar bai yarda da wannan ba, ya ce babu abin da jagororin ADC ba su yi a kan tsohon gwamnan.

Duk da suna jam’iyya guda da shi, akwai masu zargin babu kokarin da ake yi wa El-Rufai illa fitar da jawabi a aika wa ‘yan jarida.

Kokarin 'yan ADC a kan Nasir El-Rufai

Yake cewa ‘yan adawar suna tare da iyalin Malam El-Rufai domin ba su kwarin guiwa kuma suna kai masa ziyara inda yake.

Atiku yake cewa sukan aika wa juna sakonni - su tura masa shi ma ya aiko masu duk da yana hannun hukumomi a Najeriya.

“To me ka ke so mu yi? Duk abin da za a yi muna yi.

Kara karanta wannan

Atiku ya fito da cikakken tsarin dawo da tallafi don man fetur ya yi araha

"Muna ba iyalinsa goyon baya. Muna zuwa wurin shi. Muna aika masa sako, yana aika mana da sauransu.”

- Atiku Abubakar

Da aka ce masa ana zargin gwamnati tana ganin babban ‘dan adawar a matsayin barazana, shi ma ‘dan takaran ya goyi bayan wannan ra’ayi.

Atiku Abubakar ya amsa:

"Eh, tunda gwamnati ce ta marasa gaskiya, komai yana iya faruwa."

Me ya hana a iya kama Atiku Abubakar?

Da aka tambaye shi ko akwai abin da yake yi saboda gudun irin haka ta faru da shi, sai ya ce ai babu abin da zai sa gwamnati ta cafke sa.

‘Dan siyasar ya ce sirrin kyale shi da aka yi shi ne bai aikata ba daidai ba, ya ce da ya yi, da mahukunta sun dade da yin ram da shi.

“Ban yi sata ba, ban ci hakki ba, babu tabo”

Duk an ji wannan a wata tattaunawa ta musamman da aka yi da shi a Facebook Live bayan an bude kofar yakin zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar zai dawo da tallafin man fetur idan ya ci zaben 2027

Bidiyon hirar da aka yi da Atiku

Abin da El-Rufai ya fada wa Atiku

A farkon bana aka ji Mallam Nasir El-Rufai ya karbi bakuncin Atiku Abubakar a gidansa bayan jami'an tsaro sun yi yunkurin kama shi a filin jirgi.

El-Rufai ya shaida wa Atiku cewa dole ne 'yan adawa su tashi tsaye su haɗa kai domin cire gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Jim kadan da shigowa Najeriya, tsohon gwamnan ya zargi hukumomin tsaro da bari ana amfani da su ta hanyar siyasa maimakon su yi aikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng