ADC Ta Hango Abin da Zai Jawo Matsalar Yan Bindiga a Jigawa, Ta Gargadi Gwamnati
- Jam’iyyar ADC ta yi gargadin cewa faɗaɗa harkokin haƙar ma’adinai a Jigawa na iya buɗe ƙofa ga ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane
- ADC ta buƙaci a dakatar da sabbin ayyukan haƙar ma’adinai har sai an gudanar da cikakken binciken tsaro tare da samar da isassun matakan kariya
- Jam'iyyar ta ce zaman lafiyar da Jigawa ke da shi abu ne mai muhimmanci da ya kamata a kare, maimakon jira har sai ƙungiyoyin su lalata shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa – Jam’iyyar ADC, reshen Jihar Jigawa, ta yi gargadin cewa shirin gwamnatin jihar na faɗaɗa ayyukan haƙar ma’adinai na iya jefa zaman lafiyar jihar cikin haɗari.
Jam’iyyar ta ce a daidai lokacin da ake fama da matsalar tsaro da kuma matsin tattalin arziki a faɗin ƙasar, faɗaɗa harkokin haƙar ma’adinai ba tare da samar da ingantattun matakan tsaro ba, na iya jawo sabbin barazanar tsaro.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ce wannan matsayar ta biyo bayan ƙaddamar da Kwamitin Kula da Albarkatun Ma’adinai da Muhalli (MIREMCO) da gwamnatin Jigawa ta yi domin bunƙasa albarkatun ma’adinai da ƙara samun kuɗaɗen shiga.
ADC ta hango matsala a Jigawa
Peoples Gazette ta wallafa cewa a wata sanarwa da Mataimakin Shugaban ADC na Jihar Jigawa, Ambasada Nuraddeen Jidawa, ya fitar a Dutse ranar Alhamis, jam’iyyar ta ce dole ne a yi la'akari da tsaro.
Ya ce:
“Jam’iyyar ta yi gargadin gwamnati kan buɗe wata sabuwar kafa ta matsalar tsaro ba da gangan ba a jihar da ta kasance cikin kwanciyar hankali idan aka kwatanta da sauran jihohin Arewa maso Yamma.”
Jidawa ya ce manufar tsara harkokin haƙar ma’adinai da ƙara kuɗaɗen shiga abu ne mai kyau, amma tsaro ya kamata ya zo kafin hakan.
ADC ta gargadi gwamnatin Jigawa
Ya kuma yi gargadin cewa idan ba a tsara harkokin haƙar ma’adinai yadda ya kamata ba, za su iya zama hanyar da ‘yan bindiga da masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba su shiga jihar.

Source: Twitter
Akwai tsoron zai kuma jawo masu ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci, masu safarar makamai da masu fasa-kwauri za su yi amfani da ita wajen kafa sansanoni a Jigawa.
Mataimakin shugaban jam’iyyar ya ce rahotannin shigar wasu ‘yan ƙasashen waje cikin wuraren da ake fama da rikici a sassan ƙasar sun sa ya zama wajibi gwamnati ta gudanar da cikakken binciken tsaro kafin faɗaɗa ayyukan haƙar ma’adinai.
Ya ce abubuwan da suka faru a jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna sun nuna yadda haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ta jawo masu aikata laifuka tare da ƙara ta’azzara matsalolin ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, karɓar kuɗin fansa da safarar ma’adinai.
Jidawa ya ce zaman lafiyar Jigawa wata muhimmiyar kadara ce da ya kamata a kare ta hanyar ɗaukar matakan kariya tun da wuri, ba wai a jira har sai ƙungiyoyin masu aikata laifuka sun samu wurin zama ba.
Shirin gwamnan Jgiawa kan alhazai
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Jigawa ta amince da mayar wa kowane maniyyacin jihar da ya yi Hajjin 2026 N53,853, wato kusan N55,000, daga kuɗaɗen da suka yi saura.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jigawa ta mayar da Naira miliyan 44.9 na kuɗin Hajji da suka yi saura ga gwamnatin jihar domin a mika su ga alhazan da suka biya kudinsu.
Sarkin Dutse ya buƙaci gwamnatin jihar ta gina sansanin wucin gadi na dindindin domin maniyyata kafin tafiya Hajji domin taimaka masu kafin tashinsu zuwa kasa mai tsarki.
Asali: Legit.ng


