Shin da Gaske Sanata Danjuma Goje Ya Fice daga Jam'iyyar APC?
- Sanata Danjuma Goje ya yi magana kan batun ficewa daga jam'iyyar APC bayan rasa tikitin takara a zaben 2027
- Tsohon gwamnan na Gombe ya ce yana tuntubar masu ruwa da tsaki kan matakin siyasar da zai dauka
- Goje ya bukaci magoya bayansa su kasance masu biyayya ga shugabannin APC yayin da suke jiran umarninsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanatan da ke wakiltar Gombe ta Tsakiya, Danjuma Goje, ya musanta cewa ya fice daga All Progressives Congress (APC).
Sanata Danjuma Goje, wanda ke wakiltar Gombe ta Tsakiya a Majalisar Dattawa tun 2011, ya ce yana tuntubar masu ruwa da tsaki na siyasa, kuma zai bayyana matakin da zai dauka a lokacin da ya dace.

Source: Twitter
Sanata Danjuma Goje ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da magoya bayansa a gidansa da ke Gombe ranar Asabar, 22 ga watan Agustan 2026, cewar rahoton jaridar The Punch.
Me Goje ya ce kan sauya sheka?
Tsohon gwamnan ya bukace su da su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga shugabannin jam’iyyar tare da shirin bin umarninsa na karshe, jaridar Leadership ta kawo labarin.
“Kar ku saurari masu cin amana, ku koma gida, ku shirya, ku kasance masu biyayya ga shugabannin jam’iyyarmu kuma ku jira umarnina na karshe,” in ji Goje.
"A yanzu ba na ficewa zuwa wata jam’iyya, amma ina tuntubar masu ruwa da tsaki. Sai dai na yi alkawarin zan kasance tare da magoya bayana ko da na samu tikitin Majalisar Dattawa ko ban samu ba.” In ji Goje.
Rikici kan makomar Goje
Wadannan kalamai na Goje sun zo ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin makomar siyasarsa bayan ya rasa tikitin APC na takarar sanatan Gombe ta Tsakiya, sannan INEC ta cire sunansa daga jerin karshe na ’yan takarar zaben 2027.
Hakan ya kara jan hankali musamman ganin yadda jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ke kokarin ganin ta ba shi tikitin takarar sanatan Gombe ta Tsakiya.
INEC ta fitar da jerin karshe na ’yan takarar a farkon watan Agusta, amma sunan Goje bai bayyana cikin ’yan takarar kujerar sanatan Gombe ta Tsakiya ba.
Goje ya tsaya takarar fidda gwani na APC na kujerar sanatan, amma ya sha kaye a hannun wani dan takara. Rahotannin da suka fito daga zaben fidda gwani sun nuna cewa Mohammed Ahmed ne ya samu tikitin APC na Gombe ta Tsakiya.
Magoya baya sun yi tir da tsarin
Tun da farko, magoya bayan Goje sun yi watsi da tsarin yarjejeniyar da jam’iyyar ta yi wanda ya sauya shi a matsayin dan takarar APC da aka tsara zai tsaya wa mazabar.
Bangaren Goje ya kuma nuna rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da tsarin.

Source: Twitter
Sababbin kalaman tsohon gwamnan sun kara rura rade-radin makomar siyasarsa, musamman sakamakon rahotannin da ke cewa ’yan siyasar jam’iyyun adawa na kokarin jawo shi zuwa bangarensu.
Sai dai har yanzu Goje bai sanar da cewa zai bar APC ba, inda ya jaddada cewa yana tuntubar masu ruwa da tsaki kafin ya yanke hukunci.
An kafa kwamitin yakin neman zaben Tinubu a APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya nada kwamitin da zai taya shi yakin neman zaben shugaban kasa a Najeriya.
An nada Aanata Abdulaziz Yari a matsayin wanda zai jagoranci yakin zaben Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a 2027.
Asali: Legit.ng


