Nyesom Wike Ya Fadi Sanatar da Ya Kamata a Kauracewa a Zaɓen 2027

Nyesom Wike Ya Fadi Sanatar da Ya Kamata a Kauracewa a Zaɓen 2027

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi magana game da zaben 2027 musamman na sanatoci a shekara mai zuwa
  • Wike ya bukaci mazauna Abuja su ki sake zaben Sanata Ireti Kingibe, yana mai neman su zabi tsohon Sanata Philip Aduda a 2027
  • Ministan ya ce Aduda “mutumin jama’a” ne mai kwarewar wakiltar bukatun mazauna Abuja, yayin da ya zargi Kingibe da rashin ziyartar al’ummomi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bukaci mazauna babban birnin tarayya su ki sake zaben Sanata mai wakiltar Abuja, Ireti Kingibe, a 2027.

Wike ya kuma bukaci mazauna yankin su kada kuri’a ga tsohon Sanata Philip Aduda, wanda ya sha kaye a hannun Kingibe a 2023.

Wike ya bukaci yan Abuja su ki zaben Sanata Kingibe
Sanata Ireti Kingibe da Ministan Abuja, Nyesom Wike. Hoto: Sen. Ireti Kingibe, Lere Olayinka.
Source: Twitter

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake duba aikin gina hanyar Zaudna-Kaba-Kagini mai tsawon kilomita biyar, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta ba da hutu domin Maulidin Annabi Muhammad SAW

2027: Wanda Wike ya ke so a zaba

Wike, wanda ya yi wa Aduda kamfen, ya bayyana shi a matsayin “mutumin jama’a” mai kwarewar da ake bukata wajen wakiltar mazauna Abuja.

Ya bukaci mazauna Abuja su ki Kingibe, yana zargin cewa ba kasafai ake ganinta a cikin al’ummomin yankin ba.

Wike ya tambayi mazauna ko Kingibe ta taba ziyartar al’ummominsu, inda rahotanni suka ce sun amsa masa da cewa ba ta ziyarta ba.

Ya ce:

“Kun gani, Ireti ta san magana ne kawai a talabijin. Kada ku zabe ta, kuma kada ku sake sauraron ta.
“Idan da gaske take, ku gaya mata ta zo ta warware matsalolinku. Daya daga cikin matsalolin ita ce wannan hanya. Ko ba haka ba? Kuma Tinubu yana magance ta."

Yayin da yake magana da mazauna al’ummar Zaudna lokacin duba aikin, Wike ya kuma bukace su da su goyi bayan Shugaba Bola Tinubu domin wa’adin mulki na biyu.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Davido ya je har gidan Wike ya ce sun kifar da APC

Ministan ya ce yakin neman zaben shugaban kasa da na Majalisar Tarayya na 2027 ya fara yadda ya kamata, yayin da ayyukan Tinubu za su tasiri zaben.

Wike ya tuna cewa an fara aikin hanyar ne bayan mazauna al’ummomin da abin ya shafa sun yi roko lokacin kaddamar da tsohuwar hanyar Old Keffi.

Hanyar ta taso ne daga Dei Dei zuwa kasuwar kifi ta Kado, inda mazauna suka nemi gwamnati ta magance matsalolin sufuri, cewar Punch.

Ya tabbatar wa mazauna cewa za a kammala hanyar kafin karshen Disamba, domin su samu damar bikin Kirsimeti suna amfani da sabuwar hanyar.

“Na sanar da Shugaba Tinubu cewa zan zo nan, kuma ya aiko da gaisuwarsa, tare da tabbatar da cewa za a kammala hanyar kafin karshen Disamba.
“Hakan zai ba ku damar yin bikin Kirsimeti kuna amfani da hanyar da aka kammala. Za a kuma girka fitilun titi a matsayin wani bangare.
“Fitilun za su taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci a al’ummomin da abin ya shafa. Don haka, ku ci gaba da tallafa wa dan kwangilar.”

- Nyesom Wike

Kara karanta wannan

Osun: Malamin addini ya shawarci matasa su yi koyi da Davido a zaben 2027

Wike ya yi magana game da zaben Osun

A baya, an ji cewa Nyesom Wike ya ce da Shugaba Bola Tinubu ya so APC ta lashe zaɓen Osun da ƙarfi, da ya taimaka masa, kuma Adeleke ba zai iya hana nasarar ba.

Wike ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta yi amfani da ƙarfinta wajen karkatar da zaɓen Osun ba, wanda Ademola Adeleke ya lashe.

Ministan ya yi hasashen cewa zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai fi sauƙi ga Tinubu saboda ya ce jam’iyyun adawa sun raunana sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.