NDC: 'Dan Uwan Mataimakin Gwamnan Kano zai Buga da Barau a 2027
- Jam’iyyar NDC ta tabbatar da Hon. Nasiru Sule Garo a matsayin ɗan takararta na kujerar Sanatan Kano ta Arewa a zaɓen 2027
- Garo zai fafata da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, wanda ke wakiltar Kano ta Arewa a ƙarƙashin APC
- Injiniya Sunusi Danbatta ya janye takararsa, inda ya bayyana cewa zai goyi bayan Garo da sauran ‘yan takarar NDC a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam’iyyar adawa ta NDC ta tabbatar da Hon. Nasiru Sule Garo a matsayin ɗan takararta na kujerar Sanatan Kano ta Arewa a zaɓen 2027.
Wannan na zuwa ne bayan jam’iyyar ta maye gurbin Injiniya Sunusi Danbatta da Garo a matsayin ɗan takararta da ta tsayar a zaɓen.

Source: Facebook
Nigerian Tribune ta wallafa cewa a wajen taron tabbatar da Garo da aka gudanar a ofishin jam’iyyar na shiyyar Sanata a Bichi, Shugaban NDC na Jihar Kano, Hon. Usaini Isa Mai Riga, ya ce an yanke shawarar a tsanake.
Kano: NDC ta fitar da dan takarar majalisa
Jaridar Independent ta wallafa cewa NDC ta ce bayan an gudanar da shawarwari masu yawa tare da duba ƙwarewar Garo, wanda ya taɓa zama ɗan Majalisar Tarayya, ana ganin zai kai labari.
Mai Riga, wanda Mataimakin Shugaban jam’iyyar na shiyya, Alhaji Bello Ado Yandadi, ya wakilta, ya ce tabbatar da Garo ya kawo ƙarshen tsarin cikin gida da jam’iyyar ta bi wajen zaɓen ɗan takararta gabanin zaɓen.
Danbatta, wanda ya janye daga takarar, ya ce ya ɗauki matakin ne da kansa, tare da yin alƙawarin ba Garo da sauran ‘yan takarar NDC cikakken goyon baya da haɗin kai a zaɓen 2027.
NDC: Garo ya yi alkawari
Garo ya yi alƙawarin haɗa dukkan ‘yan jam’iyyar cikin harkokin tafiyar da ita tare da samar da wakilci mai inganci ga al’ummar Kano ta Arewa idan aka zaɓe shi.

Source: Facebook
Ya kuma yi kira ga masu zaɓe a faɗin mazaɓar Sanatan da su mara masa baya da kuma goyon bayan manufofin siyasa na NDC.
A karin bayanin da Kakakin NDC, Hon Yusuf Fasaha ya yi wa Legit, ya bayyana cewa Garo ya yi shekara takwas yana wakiltar jama'arsa.
"Duk da Murtala da Nasiru ubansu daya, amma ba an ba shi ba ne saboda wannan. An ba shi wannan takara ne saboda ya taba zama a majalisa, yana da mutane sannan zai tafi da jam'iyya."
Hon Fasaha ya ce akwai tabbacin APC ba za ta kai labari ba a zaben 2027 a jihar Kano, domin a ganin jam'iyyar ta tara kwararrun yan siyasa da ke tare da mutane.
NDC ta shirya kara wa da Abba
A baya, mun kawo labarin cewa 'dsan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya ce nasarar Ademola Adeleke a zaben Osun ta nuna cewa jama'a su ne siyasa.
Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo ya ce al’ummar Osun sun kare kuri’unsu tare da tabbatar da aniyarsu ta kare tsarin dimokuradiyya kuma alama ce mai kyau game da zaben 2027.
Ya bayyana cewa nasarar Adeleke alama ce da ke nuna nasarar da jam'iyyar NDC za ta iya cimmawa a zaben gwamnan Kano na 2027 inda ya ke shirin karbe shirin karbe mulki.
Asali: Legit.ng


