Atiku Ya Kalubalanci Yadda FBI Ta 'Boye' Bayanai game da Tinubu
- Atiku Abubakar ya ce bai kamata FBI ta yi amfani da “barazana ga rayuka” a matsayin dalilin boye bayanan da doka ta ba da damar bayyana wa jama’a ba
- Ya ce ‘yan Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki da ya shafi abinci, magunguna da sauran bukatun yau da kullum saboda haka kawai bukatar a yi masu bayani
- 'Dan takarar shugaban kasar Najeriya a inuwar ADC ya ce kare jami’an FBI da majiyoyinsu ba yana nufin kare gaskiya daga ‘yan Najeriya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya bukaci Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) da ta bayyana bayanan da doka ta ba da damar fita game da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Sadarwa da Jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Asabar 22 ga watan Agusta, 2026.

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito Atiku ya ce abin dariya ne idan ba don irin mawuyacin halin da Najeriya ke ciki ba, ace bayyana bayanan na iya jefa rayuka cikin hadari.
Atiku ya yi magana kan binciken FBI
Nigerian Tribune ta kawo labarin Atiku ya ce a cikin shekaru uku da rabi da Tinubu ya shafe yana mulki, manufofin tattalin arzikinsa sun sanya gwamnatin cikin barazana ga rayuwar talakawan Najeriya.
A kalamansa:
“FBI ta ce bayyana bayanan na iya jefa rayuka cikin hadari. Wadanne rayuka? Tuni ‘yan Najeriya ke mutuwa."
Atiku ya ce ‘yan Najeriya da dama sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga, yayin da wasu ke mutuwa saboda yunwa, rashin kudin biyan kudin asibiti da kuma matsin tattalin arziki.
Ya ce iyalan da a baya suke iya cin abinci sau uku a rana yanzu suna kokarin samun abinci sau daya kacal, yayin da wasu iyaye ke kasa sayen magungunan ‘ya’yansu marasa lafiya.
Atiku ya soko salon mulkin Tinubu
Ya danganta halin da ake ciki da cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi ba tare da wani ingantaccen tsari na kare talakawa daga illar hakan ba.

Source: Twitter
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce idan ya samu damar mulki, dawo da tallafin man fetur ba zai kasance abin tattaunawa ba.
“Ba zan nemi afuwa ba saboda na zabi ceton rayukan ‘yan Najeriya maimakon bin akidar tattalin arzikI."
Ya ce tallafin da yake shirin mayarwa zai kasance na musamman tare da kayyade adadinsa da kuma gudanar da bincike mai zaman kansa domin hana almundahana da karkatar da kudade.
Atiku ya ce a Najeriya karkashinsa, ba za a rika auna nasarar tattalin arziki da yawan wahalar da ‘yan kasa za su iya jurewa ba.
Tinubu: Matakin da kotun Amurka ta dauka
A baya, mun kawo labarin cewa wata kotun tarayya a Amurka ta amince FBI ta gabatar da wasu bayanan bincike da suka shafi Shugaba Bola Tinubu ga alkali domin a duba su a sirrance.
FBI ta ce ba za ta iya bayyana wasu dalilan rike bayanan a bainar jama'a ba saboda hakan na iya bayyana dabarun bincike ko jefa rayukan wasu mutane cikin hadarii.
Alkalin kotun, Beryl Howell, ta bai wa FBI, DEA, DOJ da tawagar lauyoyin Tinubu wa'adin ranar 28 ga Agusta, 2026, domin gabatar da hujjojinsu na karshe game da zargin da ake yi wa shugaban.
Asali: Legit.ng


