Kalubalen da Ke gaban Atiku kan Maganar Dawo da Tallafin Mai idan Ya Yi Nasara
- Jigon jam'iyyar APC mai mulki ya kalubalanci Atiku Abubakar da ya bayyana yadda zai samar da kudin dawo da tallafin man fetur
- Faizu Alfindiki ya ce cire tallafin man fetur ya jefa 'yan Najeriya cikin wahala, amma dawo da shi ba tare da tsarin kudin ba ba mafita ba ce
- Ya bukaci 'yan siyasa su mayar da hankali kan tace danyen mai a gida, inganta ababen more rayuwa da zuba jari domin rage farashin man fetur
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Jigon APC, Alhaji Faizu Alfindiki, ya kalubalanci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kan alkawarinsa na dawo da tallafin man fetur.
Alfindiki ya ce Atiku ya kamata ya bayyana wa 'yan Najeriya yadda zai samar da kudin tallafin ba tare da kara matsin lamba kan kudaden gwamnati ba.

Kara karanta wannan
'A baya, ina goyon bayan cire tallafi': Atiku ya fadi dalilin sauya tunani kan lamarin

Source: Twitter
Ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano ranar Juma'a, yana mai cewa 'yan Najeriya na bukatar cikakken bayani kan tsarin kudin, cewar Vanguard.
Tallafin mai: Jigon APC ya kalubalanci Atiku
Martanin nasa ya biyo bayan alkawarin Atiku na dawo da tallafin man fetur, inda ya ce har yanzu 'yan Najeriya ba su ga isasshen amfani daga kudaden ba.
Alfindiki ya ce yana da kyau 'yan Najeriya su tambayi yadda ake tafiyar da kudaden gwamnati, amma dawo da tallafin ba tare da bayyana hanyar daukar nauyinsa ba ba mafita ba ce.
Ya ce:
“Yana da kyau a tambayi yadda ake tafiyar da kudaden gwamnati, amma yana da muhimmanci a fahimci illar tattalin arziki da komawa tsarin tallafin man fetur ke haifarwa”.
Ya kara da cewa 'yan Najeriya na bukatar hanyoyin magance matsaloli masu dorewa, ba manufofin da aka tsara musamman domin samun nasarar muhawarar siyasa ba.

Source: Facebook
Alfindiki ya fayyace tsarin samar da kuɗin tallafi
Alfindiki ya kuma tambayi dalilin sauyin ra'ayin Atiku, yana mai cewa a yakin neman zaben shugaban kasa na 2023, Atiku ya yi alkawarin cire tallafin.
Ya ce Atiku ya bayyana cewa zai cire tallafin man fetur cikin kwanaki 100 na farko idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, cewar Punch.
Ya ce:
“Yanzu Atiku yana gabatar da dawo da tallafin a matsayin mafita, alhali kafin zaben 2023 matsayinsa shi ne a cire tallafin”.
Ya kara da cewa 'yan Najeriya suna da damar tambayar abin da ya sauya da kuma dalilin da ya sa Atiku ya canza matsayinsa kan batun.
Alfindiki ya bukaci shugabannin siyasa su daina mayar da hankali kan takaddamar ko tallafin man fetur ya kasance ko a'a.
A maimakon haka, ya ce ya kamata a mai da hankali wajen gina tattalin arzikin da zai sa man fetur ya kasance mai saukin kudi ga 'yan Najeriya.
Tallafin mai: Atiku ya fadi dalilin sauya tunani
An ji cewa Atiku Abubakar ya sauya matsayinsa kan tallafin man fetur, inda ya ce zai dawo da shi idan aka zabe shi shugaban Najeriya a 2027.
Mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya kare matakin, yana cewa shugaba mai tausayi ya kamata ya sake duba manufofin da suke jefa jama'a cikin wahala.
Ibe ya ce shirin Atiku zai rage farashin tace man fetur a cikin gida, wanda zai saukaka sufuri, noma, masana'antu da sauran harkokin tattalin arziki.
Asali: Legit.ng

