Najeriya, Wasu Kasashe Sun Samu Sauki, Alkalin Amurka Ya Soke Hukuncin Trump
- Wata kotun Amurka ta soke dokar gwamnatin Trump da ta dakatar da bayar da bizar ga wasu ƙasashe har 75
- Alkalin kotun, Jeannette Vargas, ta ce dokar ta saba wa dokokin shige da fice na Amurka, domin ta wuce ikon ministan harkokin waje
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce mutanen ƙasashen suna kawo cikas ga tallafin arzikin gwamnatin kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Wata alkalin kotun Amurka a ranar Juma’a ta yi karan tsaye kan wata dokar gwamnatin Shugaba Donald Trump.
Dokar ta dakatar da bayar da bizar ƙaura ga masu neman shiga Amurka daga ƙasashe 75 ciki har da Najeriya.

Source: Getty Images
Hukuncin alkalin kotun Amurka
Alkalin Kotun Gundumar Amurka da ke Manhattan, Jeannette Vargas, ta ce manufar da Ma’aikatar Harkokin Waje ta sanar a watan Janairu ta kasance “ba bisa doka ba”, cewar France24.
Ta ce manufar ta wuce ikon da doka ta bai wa Ministan Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, musamman kan yadda jami’an ofishin jakadanci ke gudanar da harkokin bizar ƙaura.
Vargas ta ce:
“Manufar, wadda ta haramta bayar da bizar ƙaura bisa asalin ƙasar mai neman bizar, ta saba kai tsaye da tsarin da doka ta tanada.”
Matakin Ma’aikatar Harkokin Wajen ya shafi masu neman biza daga ƙasashe daban-daban a Latin Amurka, ciki har da Brazil, Colombia da Uruguay.
Haka kuma ya shafi ƙasashen Balkan kamar Bosnia da Albania, da ƙasashen Kudancin Asiya irin su Pakistan da Bangladesh, tare da wasu ƙasashe da dama a Afirka, Gabas ta Tsakiya da Caribbean.
Ma’aikatar Harkokin Wajen ta ce masu neman biza daga ƙasashen da abin ya shafa suna cikin “babban haɗarin zama nauyi ga jama’a” da kuma dogaro da albarkatun gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi a Amurka.
Sai dai Ma’aikatar Harkokin Wajen ba ta bayar da wani martani nan take kan hukuncin kotun ba.
Vargas, wadda tsohon Shugaban Amurka Joe Biden ya naɗa, ta yanke hukuncin ne bayan ƙungiyoyin kare haƙƙin ’yan ƙaura sun shigar da ƙara.

Source: Getty Images
Ƙasashe 75 da dokar ta shafa a duniya
Ƙasashen su ne Najeriya, Afghanistan, Albania, Algeria, Antigua and Barbuda, Armenia, Azerbaijan, Bahamas, Bangladesh, Barbados, Belarus, Belize, Bhutan, Bosnia and Herzegovina, Brazil, Burma, Cambodia, Cameroon, Cape Verde, Colombia, Cote d’Ivoire, Cuba, Democratic Republic of the Congo, Dominica, Egypt, Eritrea, Ethiopia, Fiji, The Gambia, Georgia, Ghana, Grenada, Guatemala da Guinea.
Sauran ƙasashen sun haɗa da Haiti, Iran, Iraq, Jamaica, Jordan, Kazakhstan, Kosovo, Kuwait, Laos, Lebanon, Liberia, Libya, Moldova, Mongolia, Montenegro, Morocco, Nepal da Nicaragua.
Haka kuma akwai Pakistan, Republic of the Congo, Russia, Rwanda, Saint Kitts and Nevis, Saint Lucia, Saint Vincent and the Grenadines, Senegal, Sierra Leone, Somalia, South Sudan, Sudan, Syria, Tanzania, Thailand, Togo, Tunisia, Uganda, Uruguay, Uzbekistan da Yemen.
Rahoton ya nuna cewa dukkan ƙasashen 75 suna Afirka, Asiya, Latin Amurka, Gabas ta Tsakiya da Gabashin Turai, inda yawancin al’ummominsu ba farare ba ne ko kuma suke da manyan ƙananan ƙabilu, cewar Punch.
Amurka ta santa takunkumi ga wasu yan Najeriya
A baya, an ji cewa Amurka ta fara daukar matakai da nufin kawo karshen kisan kiyashin da take zargin ana yi wa kiristoci a Najeriya da wasu kasashe.
A wata sanarwa da ma'aikatar wajen Amurka ta fitar, ta hana bada biza ga wadanda ke da hannu a ayyukan tauye 'yancin addini.
Ta jaddada cewa kamar yadda Shugaba Donald Trump ya fada, Amurka za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare rayukan kiristoci a duniya.
Asali: Legit.ng


