Amurka Ta Sake Tono Rigima, Ta Yi Sabon Wulakanci ga Iran
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce ta kori mambobin tawagar Iran biyu daga ƙasar bayan sun ƙi bin umarnin barin Amurka
- Jami’an Iran sun halarci babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya na baya-bayan nan a New York kafin su ci gaba da zama a ƙasar
- Matakin ya zo ne yayin da Washington da Tehran ke ci gaba da samun saɓani kan tattaunawar diflomasiyya da batun mashigar Hormuz
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Amurka ta kori mambobin tawagar Iran biyu da suka halarci babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya na baya-bayan nan bayan sun ƙi bin umarnin barin ƙasar.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ce ta bayyana hakan ranar Asabar, 3 ga watan Oktoban shekarar 2026.

Source: Getty Images
Tashar Roya News ta ce wani jami’in Amurka ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an gano wasu mambobin tawagar Iran biyu har yanzu suna New York, duk da cewa taron Majalisar Ɗinkin Duniya ya ƙare tun da daɗewa.
Ya ce “Yanzu an kore su daga Amurka,” yana mai cewa Ministan Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, “da gaske yake” kan batun.
An umarci tawagar Iran ta bar Amurka
Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ruwaito cewa Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar ta umarci Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, da tawagarsa su bar Amurka ranar Litinin.
Sai dai an gano daga ofishin wakilan Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya ranar Juma’a cewa wasu daga cikin mambobin tawagar har yanzu suna ƙasar.
A cewar jami'in, ɗaya daga cikin jami’an ya bar Amurka a daren Juma’a, yayin da na biyu ya bar ƙasar safiyar Asabar, 3 ga watan Oktoban 2026.
Jami’an Amurka da Iran sun gana a New York
Jami’an Amurka da Iran sun gana a makon da ya gabata a New York, a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ganawar ta zo ne a lokacin da ake ci gaba da samun rashin jituwa tsakanin Washington da Tehran kan batutuwan diflomasiyya da kuma makomar tattaunawar tsakanin ƙasashen biyu.

Kara karanta wannan
Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027
Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙi amincewa da wata shawarar da Tehran ta gabatar kan sake buɗe mashigar Hormuz.
Sai dai Trump ya shaida wa kafofin yaɗa labaran Amurka cewa yana sa ran a ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu a cikin kwanaki masu zuwa.
Iran ta ce babu sabon taron tattaunawa
A gefe guda, kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran, IRNA, ya ruwaito cewa Tehran ba ta da wani sabon shirin gudanar da tattaunawa kai tsaye da Washington a halin yanzu.
Hakan na zuwa ne yayin da dangantakar Amurka da Iran ke ci gaba da kasancewa cikin yanayi mai sarkakiya, musamman kan batutuwan diflomasiyya da tsaro.

Source: Getty Images
Trump ya yi barazana ga Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasae Amurka, Donald Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari mai tsanani.
Trump ya yi barazanar kai harin ne idan aka tabbatar da cewa tana da hannu a wani lamari da ya shafi jirgin FlyDubai da ke kan hanyarsa daga Dubai zuwa Tel Aviv.
Asali: Legit.ng
