'A Guji Siyasantar da Tsaro': Ɗan APC Ya Koɗa Ministan Tsaro kan Yaƙi da Ta'addanci
- Ana ci gaba da caccakar masu yada maganar murabus din ministan tsaro, Christopher Musa a mukaminsa
- Wani masoyin Bola Tinubu, Khamis Musa Darazo ya bukaci 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki su daina siyasantar da batun tsaro
- Darazo ya yabawa Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, saboda jajircewa wajen yaki da ta'addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Wani matashi ya yabawa ministan tsaro a Najeriya, Christopher Musa a kokarinsa na yaki da ta'addanci.
Khamis Musa Darazo, daya daga cikin fitattun masu goyon bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci shugabannin siyasa, 'yan Najeriya su daina siyasantar da batun tsaro.

Source: Twitter
Darazo ya bayyana haka ne a wata zantawa da wakilin Legit Hausa inda ya yabawa Christopher Musa bisa kokarinsa.
Shawarar da aka ba yan Najeriya
Matashin ya ce matsalolin tsaron kasar na bukatar hadin kai da goyon bayan kowa domin shawo kansu.
Darazo ya bayyana cewa yaki da ta'addanci, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka na bukatar cikakken hadin kai da jajircewar dukkan 'yan Najeriya.
Ya ce karkashin ajandar Renewed Hope ta shugaban kasa Tinubu, jami'an tsaro sun samu nasarori masu yawa ta hanyar kara kai hare-hare kan miyagu, kubutar da mutanen da aka sace da kuma kwato makamai da alburusai.
Darazo ya yabawa Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, bisa jajircewa, kwarewa da sadaukarwa wajen kare Najeriya.
Ya bayyana shi a matsayin shugaba mai kishin kasa wanda kokarinsa ke taimakawa wajen samun ci gaba a yaki da rashin tsaro.
A cewarsa, bai kamata a sadaukar da batun tsaron kasa saboda bambance-bambancen siyasa ba.
Matashin ya ce wannan lokaci ne da ya dace duk masu kishin kasa su mara wa wadanda ke kare Najeriya baya.
Ya kara da cewa Janar Christopher Gwabin Musa da sauran jami'an tsaro sun cancanci karfafa musu gwiwa, hadin kai da cikakken goyon bayan kasa maimakon jefa su cikin cece-kuce na siyasa.

Source: Facebook
Darazo ya ba yan siyasa shawara kan tsaro
Darazo ya ce ingantuwar tsaro a wasu sassan Najeriya na kara dawo da amincewar jama'a, yana farfado da harkokin tattalin arziki, bunkasa noma da kuma samar da yanayi mai kyau ga zuba jari da ci gaban kasa.
Ya bukaci 'yan siyasa da masu rike da mukaman gwamnati su rika yin taka-tsantsan yayin magana kan batutuwan tsaro, tare da fifita muradun kasa sama da bukatun siyasa.
Haka kuma ya roki 'yan Najeriya su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanan sirri cikin lokaci domin taimakawa ayyukan da suke gudanarwa, yana cewa zaman lafiya mai dorewa ba zai samu ba sai da hadin kan kasa baki daya.
A karshe, Darazo ya sake bayyana cikakken kwarin gwiwarsa kan kudirin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na kara karfafa tsarin tsaron Najeriya.
Ya ce hadin gwiwar gwamnati, hukumomin tsaro da al'umma zai ci gaba da samar da sakamako mai kyau
Bala Wunti: An ba Tinubu shawara
A baya, an ji cewa wanda ya nemi takarar gwamnan Bauchi a karkashin APC, Bala Mai Jama'a Wunti na ci gaba da samun goyon bayan matasa.
Wani matashi mai suna Ahmad Gamji ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ba Dr. Bala Wunti babban mukami saboda gogewa da ƙwarewarsa.
Ya ce basira, gogewa da karɓuwar Dr. Bala Wunti a wajen jama'a sun sa ya cancanci jagoranci domin bunƙasa harkar mai da tattalin arziki.
Asali: Legit.ng


