Allah Ne Ya Saka Mun Shiyasa Tinubu Ya Samu Nasara, In Ji Oyetola

Allah Ne Ya Saka Mun Shiyasa Tinubu Ya Samu Nasara, In Ji Oyetola

  • Tsohon gwamnan Osun kuma ministan Tinubu ya bayyana matsayarsa kan korar jiga-jigan tsagin Aregbesola daga APC
  • Adegboyega Oyetola ya ce yana goyon bayan kora da dakatar da jiga-jigan mambobin APC sama da 100 a jihar
  • A kwanan bayan APC reshen jihar Osun ta kori mambobinta 84, daga bisani kuma ta dakatar da wasu 25

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Osun - Ministan tattalin arziƙin ruwa, Adegboyega Oyetola, ya bayyana cewa jam'iyyar APC reshen jihar Osun ta fara ɗaukar matakan tsaftace kanta ta hanyar korar bara gurbi.

Jaridar Punch ta rahoto cewa a baya-bayan nan, jam'iyyar APC ta kori tsohon shugaban tsagi ɗaya, Rasaq Salinsile, da wasu jiga-jigai 83 da ke goyon bayan tsohon gwamna, Rauf Aregbesola.

Ministan ruwa da tattalin arziƙi, Oyetola.
Allah Ne Ya Saka Mun Shiyasa Tinubu Ya Samu Nasara, In Ji Oyetola Hoto: Adegboyega Oyetola
Asali: Facebook

Haka nan kuma jam'iyyar ta dakatar da tsohon sakataren gwamnatin jihar, Moshood Adeoti, da wasu mambobi 25 bisa zargin cin amana da zagon ƙasa.

Kara karanta wannan

"Kowace Jiha 1,000" Shugaba Tinubu Ya Amince da Muhimmin Aiki a Jihohi 7 Na Arewacin Najeriya

Ministan ya tsoma baki kan matakin da APC ta ɗauka

Oyetola ya yi bayanin cewa yana goyon bayan matakin kora da dakatarwan da aka yi wa mambobin APC kana ya roƙi sauran masu kishin jam'iyya su yi aiki tukuru domin sake gina APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya yi wannan furucin ne a Osogbo, babban birnin Osun ranar Alhamis a wurin liyafar da aka shirya ta musamman domin karrama shi, rahotanni sun tabbatar.

Mista Oyetola ya ce:

"Muna ƙara godiya ga Allah bisa nasarorin da ya bamu, muna ƙara gode wa Allah bisa tabbatar da nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda Kotun zaɓe ta yi ranar Laraba."
"A baya muna ta fafutukar neman tazarce amma Allah ya san lokacin mu bai yi ba. Ya bamu shugaban ƙasa wanda ga shi a yau ya naɗa ni a matsayin Minista, ina farin ciki APC ta dunƙule wuri ɗaya."

Kara karanta wannan

Tinubu: Gwamnan PDP Ya Manna Hotonsa a Jikin Buhunan Shinkafa, Ya Faɗi Dalili

"Mun fara tankaɗe da rairaya domin banbanta aya da tsakuwa kuma da ikon Allah jam'iyyar mu zata dawo da ƙarfinta. Jam'iyyar APC ta kowanen mu ce, mu riƙe ta gam-gam."

Rigimar Jam'iyyar NNPP Ta Ɗauki Sabon Salo

A wani rahoton na daban Rigimar da ta tsaga jam'iyyar NNPP gida biyu ta ɗauki sabon salo yayin da tsagin Kwanmwaso ya fara ɗaukar matakai masu tsauri.

Tsagin NNPP mai goyon bayan Kwankwaso sun fara yunkurin sauya tambarin jam'iyyar da kuma garambawul ga kundin mulkin NNPP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel