Abdulaziz Ganduje: Ana Rade Radin Yaron Shugaban APC, Ya Fita Zakka da Shiga Jam’iyyar NNPP

Abdulaziz Ganduje: Ana Rade Radin Yaron Shugaban APC, Ya Fita Zakka da Shiga Jam’iyyar NNPP

  • Wasu mabiya Kwankwasiyya kuma masoyan NNPP sun ce Abdulaziz Abdullahi Umar Ganduje ya shigo jam’iyya mai kayan dadi
  • Idan ta tabbata, yaron tsohon gwamnan na Kano zai kunyata mahaifinsa watau Abdullahi Ganduje wanda yake rike da APC
  • Abdulaziz Ganduje ya ziyarci wani shugaba a jam’iyyar NNPP, kwanakin baya kuma an ga shi tare da Rabiu Musa Kwankwaso

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Zuwa yanzu wasu daga cikin mabiya darika Kwankwasiyya, suna ta yamadidi da labarin babban kamu da suka yi a siyasa.

A safiyar Laraba, 8 ga watan Nuwamba 2023, Ibrahim Adam, wanda hadimi ne ga Rabiu Musa Kwankwaso, ya fito da wata sanarwa.

Malam Ibrahim Adam ya fito shafinsa na Twitter ya na cewa Alhaji Abdulaziz Abdullahi Umar Ganduje ya zama ‘dan jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Kwadayi Ya Jawo Mana: Jagora a PDP Ya Fadi Wadanda Su ka Yi Sanadiyyar Fadi Zabe

Abdulaziz Ganduje
Abdulaziz Ganduje a ofishin NNPP Hoto: Ibrahim Adam
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahaifin Abdulaziz Ganduje shi ne Shugaban APC

Abdulaziz Abdullahi Umar Ganduje shi ne babban yaron shugaban jam’iyyar APC na kasa watau Dr. Abdullahi Umar Ganduje a Duniya.

Hadimin jagoran na NNPP kuma ‘dan takaran shugaban Najeriya a zaben 2023, ya wallafa hotunan da ke nuna cigaban da aka samu.

Hotuna sun nuna Abdulaziz Ganduje ya fito daga motarsa, daga nan aka kai shi gaban wani jagora a NNPP a satakariyar jam’iyyar.

Legit ba ta iya tabbatar da gaskiyar wannan labari ba, kuma ba mu da masaniya game da wanda yaron tsohon gwamnan ya gana da shi.

Sai dai kafin yanzu, majiyarmu ta shaida mana Abdulaziz Ganduje ya kai ziyara zuwa gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a garin Kano.

Kwankwaso wanda yanzu ya na kasar Misra, shi ne shugaban tafiyar Kwankwasiyya kuma wanda ya fito da jam’iyyar NNPP a 2023.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi martani ga babatun Obi kan kotun koli, ya fadi dalilin da ya sa aka ki shi a zabe

Ganduje: Barewa ta yi gudu, 'da ya yi rarrafe

Wannan labari ba zai ba mutane da yawa mamaki ba domin da alama Abdulaziz Ganduje ya raba jiha da mahaifinsa a tafiyarsu ta siyasa.

'Danuwansa Umar Ganduje ya yi takara a APC, amma NNPP ta doke shi. Fatima Ganduje kuwa ta yi aiki da Femi Gbajabiamila a majalisa.

Abdulaziz Ganduje v Hafsat Ganduje

A yayin da sauran ‘yanuwansa su ke goyon bayan APC, Abdulaziz Ganduje ya taba samun sabani da mahafiyarsa, har batun ya je ga EFCC.

A lokacin an ji cewa akwai yiwuwar Abdulazeez Ganduje ya yi shari’a a kotu da Gwamnatin mahaifinsa a jihar Kano saboda kwangila.

Asali: Legit.ng

Online view pixel