Umahi: A Karshe, Ministan Tinubu da Aka Tsinci Gawar Budurwa a Gidansa Ya Fadi Abin da Ya Faru

Umahi: A Karshe, Ministan Tinubu da Aka Tsinci Gawar Budurwa a Gidansa Ya Fadi Abin da Ya Faru

  • Ministan ayyuka, David Umahi ya yi magana kan mutuwar wata ma'aikaciyar jinya da ke aiki a gidansa na jihar Ebonyi
  • Lamarin mutuwar Mary Habila ya dauki hankali a yan kwanakin nan, inda wasu suka fara neman ministan ya yi murabus
  • David Umahi ya bukaci iyalan marigayiyar su amince a yi mata gwajin gawa domin tabbatar da abin da ya yi ajalinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ministan Ayyuka, David Umahi, ya karya shirunsa kan mutuwar hadimarsa, Mary Habila, wadda ta rasu a gidansa da yake saukar baƙi a Uburu, jihar Ebonyi.

Umahi ya ce ba ya zargin an aikata wani laifi kan marigayiyar, yana mai cewa kokarin alakanta shi da lamarin siyasa ce da ta wuce gona da iri.

Umahi.
Ministan Ayyuka na Najeriya, David Umahi yana jawabi a wurin taro a Abuja Hoto: David Umahi
Source: Twitter

Umahi ya fadi alakarsa da Mary Habila

Kara karanta wannan

Mary Habila: Sababbin bayanai sun fito kan mutuwar budurwa a gidan Ministan Tinubu

Punch ta ruwaito cewa da yake magana da manema labarai a Abuja, Umahi ya ce marigayiyar ta shafe kusan shekara uku tana aiki tare da shi, kuma ya dauke ta tamkar ɗiyarsa.

Ya bayyana cewa Mary ma'aikaciyar jinya ce a Jami'ar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Ebonyi, ba kwararriyar mai ilimin tausa ba kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.

Umahi ya ce:

"Mary tamkar 'yata ce. Ta zauna tare da ni tsawon shekara uku. Ita ma'aikaciyar jinya ce kuma iyalinta da namu tamkar iyali daya ne."

Ministan ya fadi rashin lafiyarta

Ministan ya bayyana cewa marigayiyar tana fama da rashin lafiya tun kafin rasuwarta, kuma ya kasance yana biyan kudin maganinta.

A cewarsa, ta samu kulawa a wani asibitin Turkiyya, inda ya ce kudin jinyar da ya biya na baya-bayan nan ya kai Naira miliyan 2.2.

Umahi ya ce kafin mutuwarta, Mary ta yi magana da saurayinta ta wayar tarho inda ta shaida masa cewa tana zubar jini daga hanci.

Yadda aka tsinci gawar Mary Habila

Ya ce saurayin ya bukace ta ta sanar da shi ko kuma ta je asibiti, amma daga baya ya katse kiran saboda gudun kada hakan ya kara zubar jinin.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi yadda Kiristoci suka karbi tikitin Muslim Muslim a Najeriy

A cewarsa:

"Bayan mintuna uku, saurayin ya sake kiranta amma ba ta amsa ba."

Umahi ya ce bayan an kasa samun amsa daga gare ta, aka fasa kofar dakinta inda aka tarar da ita ta rasu, yayin da famfon ruwa ke ci gaba da gudana.

Ya jaddada cewa gidan da lamarin ya faru yana nesa da gidansa, don haka bai dace a dora masa alhakin abin da ya faru ba.

Mary.
Ma'aikaciyar jinya, Mary Habila, wacce ta mutu a gidan ministan ayyuka, David Umahi Hoto: Mary Habila
Source: Getty Images

Umahi ya bukaci a yi gwajin gawa

Ministan ya bayyana cewa ya umurci kada a yiwa marigayiyar jana'iza har sai an yi gwajin gawa domin gano hakikanin musabbabin mutuwarta, amma iyalanta sun nuna rashin amincewa saboda al'adarsu.

Umahi ya ce ya bukaci Sufeto Janar na 'Yan Sanda ya mayar da binciken zuwa Abuja domin gudanar da cikakken bincike tare da shawo kan iyalan su amince da gwajin gawar.

Matakin da yan sanda suka dauka

Kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta jihar Ebonyi ta bukaci a gudanar da binciken gawa bayan an sami gawar Mary Habila, mai shekaru 26, a gidan Ministan Ayyuka, David Umahi.

Kara karanta wannan

'Umarnin boka ne': Makashin Fatima da yaranta 6 ya fara yi wa kotun Kano bayani

Binciken farko ya nuna cewa Habila tana cikin tawagar ma'aikatan lafiya da suka raka Umahi zuwa gidansa, inda ta rasu a wani daki da ke cikin gidan.

Duk da yake cewa rundunar ta shirya dauko kwararren likitan bincikenMgawa domin gudanar da aikin, iyalan Mary Habila sun ki amincewa da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262