Shugaba Buhari Ya Maida Tsohon Hadiminsa, Bashir Ahmad, Ya Ba Shi Babban Matsayi

Shugaba Buhari Ya Maida Tsohon Hadiminsa, Bashir Ahmad, Ya Ba Shi Babban Matsayi

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sake naɗa tsohon hadiminsa, Bashir Ahmad, a wani babban matsayi da ya zarce na baya
  • Mista Ahmad ya yi murabus daga matsayin mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin kafafen sada zumunta don ya tsaya takara a Kano
  • Sai dai ya sha kaye a zaɓen fidda gwanin ɗan majalisar mai wakiltar Gaya/Ajingi/Albasu, ya ce ba'a masa adalci ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhati, ya naɗa tsohon mai taimaka masa kan harkokin kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad, a matsayin babban mai taimaka masa na musamman kan sadarwar zamani.

Hukumar Dillancin labarai ta kasa (NAN) ta rahoto cewa Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya tabbatar da naɗin da wata takardar ɗaukar aiki da ya aike wa Bashir Ahmad, ranar 20 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun yi Ram da Shugaban Dalibai Bayan Yace Minista Bai yi Wanka ba Ya Gana da Shugaban Kasa

Buhari da Bashir Ahmad.
Shugaba Buhari Ya Maida Tsohon Hadiminsa, Bashir Ahmad, Ya Ba Shi Babban Matsayi Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

A takardar wacce NAN ta ci karo da ita ranar Lahadi a Abuja, Mustapha ya ce naɗin ya fara aiki ne daga ranar 19 ga watan Yulu, 2022.

Meyasa ya aje aiki tun farko?

Premium Times ta tattaro cewa Mista Ahmad ya yi murabus daga kan kujerarsa ta baya ne domin cika umarnin shugaban ƙasa, inda ya roki baki ɗaya masu rike da naɗin siyasa da ke niyyar tsayawa takara su aje aiki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hadimin shugaban kasan ya sha kaye a zaben fidda gwanin APC, inda ya nemi tikitin takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Gaya/Ajingi/Albasu a majalisar dokoki ta ƙasa.

Ahmad ya nuna bacin ransa kan yanayin yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwanin, inda ya ce zaɓen cike yake da ha'inci da zamba.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Bashir Ahmad ne kaɗai hadimin shugaban ƙasa da Buhari ya sake mayar wa kan wani muƙami tun bayan kammala zaɓen fidda yan takarar APC.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Naɗa Habiba Lawal a Wani Babban Matsayi Cikin Hadimansa

Baki ɗaya mambobin majalisar zartarwan Buhari, Ministoci da hadimai banda Ahmad, waɗan da suka yi murabus domin tsaya wa takara, tuni shugaban ƙasan ya maye gurbin su, daily trust ta ruwaito.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya naɗa tsohon Ɗan majalisar tarayya daga Kano a wani babban matsayi

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya naɗa tsohon ɗan majalisar tarayya, Nasiru Ila, a matayin mai taimaka masa kan harkokin majalisa.

Mista Ila zai hau kujerar da Umar El-Yaƙub ya bari bayan shugaban ya naɗa shi Minista a baya-bayan nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel