Hotuna: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya lale N10m, ya siya fom din takarar majalisar wakilai

Hotuna: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya lale N10m, ya siya fom din takarar majalisar wakilai

  • Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya lale N10 miliyan inda ya siya fom din takarar kujerar majalisar wakilai karkashin jam'iyyar APC
  • A wallafar da yayi a shafinsa na Twitter, ya sanar da cewa ya cike bangarensa na fom din kuma yana fatan wakiltar Gaya, Ajingi da Albasu a majalisar wakilai
  • Ba kamar sauran 'yan takara ba, Bashir Ahmad bai bayyana siyan fom din yayi da kudinsa ba ko wata kungiya ce ta siya masa

Kano - Mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a fannin yada labarai da sadarwa mai dogaro da fasahar zamani, Bashir Ahmad, ya siya fom din takarar kujerar majalisar wakilai.

Ahmad, wanda ke son wakiltar mazabar gaya, Ajingi da Albasu a majalisar wakilan kasar nan, ya lale N10 miliyan ya siya fom din a cikin ranakun karshen makon nan.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Kano: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya lale N10m, ya siya fom din takarar majalisar wakilai
Kano: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya lale N10m, ya siya fom din takarar majalisar wakilai. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Zai kara takarar da dan majalisar wakilan yankin mai ci yanzu, Mahmoud Abdullahi Gaya, wanda shi ma dan jam'iyyar APC ne.

Ahmad yana daya daga cikin hadiman shugaba Buhari masu karancin shekaru. An nada shi mukaminsa a lokacin da ya ke da shekaru 24 bayan kwashe shekaru da yayi yana aikin jarida.

Ba kamar sauran 'yan takara da ke bayyana wadanda suka siya musu fom ba, Ahmad bai bayyana ko wata kungiya ta siya masa fom din ba ko kuma da kansa ya siya.

A yayin bayyana labarin a shafinsa na Twitter, Ahmad ya ce, "Yanzu na kammala cike bangaren nawa a fom din, sauran kuma 'yan mazaba ta za su cike, mutanen kirki na kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu wadanda da izinin Allah zan wakilta a majalisar wakilai. Ina fatan Allah SWT ya ba mu nasara."

Kara karanta wannan

Jonathan Zai Yi Takarar Shugaban Ƙasa a 2023, Ya Yi Rajista Da APC a Mazabansa, Majiya

Ganduje ya raba gardamar APC a Kano, ya tsaida wanda zai gaje kujerarsa a zaben 2023

A wani labari na daban, mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasir Gawuna shi ne wanda ake tunanin zai rike tutar APC a zaben gwamnan Kano da za ayi a 2023.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Lahadi, 8 ga watan Mayu 2022 da ya bayyana cewa Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya tsaida zabinsa.

Mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ayyana Nasir Gawuna ne a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel