Yadda Gombe, Borno da Jihohi ke Kokarin Rage Kudin Sufuri ga Talakawa
- Gwamnatin Tarayya ta ƙara matsa lamba domin ganin an rage kuɗin sufuri daga 1 ga Oktoba, yayin da jihohi ke amfani da hanyoyi daban-daban wajen aiwatar da shirin CNG
- Yayin da wasu jihohi ke samar da motocin sufuri masu rangwame, masu motocin haya a wasu jihohin na kokawa kan ƙarancin tashoshin CNG, tsadar sauya mota da sauransu
- Matsalolin sun janyo tambayoyi kan ko gwamnati da masu sufuri za su iya cimma burin rage kuɗin sufuri a faɗin ƙasar cikin wa'adin da Shugaba Bola Tinubu ya sanya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Yayin da Gwamnatin Tarayya ke shirin ganin an samu raguwar kuɗin sufuri daga 1 ga Oktoba, jihohin Najeriya na ɗaukar matakai daban-daban domin amfani da CNG wajen rage kuɗin sufuri.

Kara karanta wannan
Tinubu ya sanar da karyewar farashin sufuri a Najeriya, ya kafa hujja da Kaduna da wasu jihohi
Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin aiwatar da shirin bayan ganawarsa da gwamnonin jihohi 36 a ranar 27 ga Agusta.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cea kwamitin na ƙarƙashin ƙungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, kuma Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ne ke jagoranta.
Yanayin shirin CNG a jihohi
A Jihar Plateau, gwamnatin jihar ta ce tana samar da ɗaya daga cikin motocin sufuri na cikin gari masu rahusa a ƙasar ta hanyar shirinta na tallafa wa jama'a.
A Kaduna kuwa, shirin CNG ya zama wani ɓangare na tsarin sufuri na jama'a, inda gwamnatin jihar ta ce motocin bas na CNG kyauta suke aiki tun watan Yulin 2025.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al'adu na jihar, Malam Ahmad Mayaki, ya ce motocin na aiki ne a hanyoyi takwas da tashoshin tsayawa kusan 200.
Gombe na bukatar ƙarin tashoshi
A Jihar Gombe, wani ma'aikacin harkar sufuri ya ce jihar na da CNG, amma kayan aikin ba su isa ba musamman wajen zirga-zirgar dogon zango.
Ya ce mutum da ke son tafiya Abuja ya dawo washegari na iya shafe sa'o'i shida, bakwai ko takwas yana jiran cike CNG saboda ƙarancin tashoshin.

Kara karanta wannan
"Ku nemi mafaka," NiHSA ta jero jihohi 15 da za a yi mummunar ambaliyar ruwa a Najeriya
Ya ce akwai shirin samar da kusan tashoshin CNG 30 a faɗin Gombe, inda ake sa ran samun ɗaya a kowace hedikwatar ƙaramar hukuma.
Ya kuma ce tsadar sauya mota zuwa CNG na daga cikin manyan abubuwan da ke hana jama'a shiga shirin, musamman a Arewa.
Shugaban tashar Gombe Line, Dr Sani Sabo, ya ce shirin CNG na da damar rage kuɗin sufuri da na man fetur, amma ƙara samar da abubuwan more rayuwa zai ɗauki lokaci.
Matsalar CNG a Jigawa
A Jihar Jigawa, masu motocin haya sun ce zai yi wahala a cimma burin rage kuɗin sufuri ba tare da samar da tashoshin CNG da cibiyoyin sauya motoci ba.
Wani jami'in NATO, Muhd Mudi, ya tambayi inda masu motocin jihar za su samu gas idan babu isassun tashoshin CNG.
A Zamfara kuma, masu abubwan hawa sun ce har yanzu jihar ba ta da tashar CNG, lamarin da ke jinkirta amfanin shirin ga mazauna jihar.
Wani direban mota, Aminu Suleiman, ya ce shirin na iya rage wahalhalun da tashin farashin man fetur ya jawo, amma ya nuna fargabar cewa jihar ba ta ga CNG ba duk da yawan alkawurran da aka yi.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Source: Twitter
Matsalar CNG a Kwara
Rahoto ya nuna cewa a Jihar Kwara, adadin motocin da aka sauya zuwa CNG har yanzu bai yi yawa ba.
Shugaban RTEAN, na jihar, Abdulrasheed Onikijipa, ya ce kusan motocin haya 100 ne kawai na mambobinsu aka sauya zuwa CNG.
Ya ce wasu masu motocin na guje wa shirin saboda rashin amincewa da tsarin da kuma zargin cewa CNG na iya lalata motocinsu.
A Borno kuwa, wasu masu sufuri sun ce tsoron matsalar tsaro da kuma farashin gas na hana wasu masu motoci rungumar shirin CNG.
Tinubu ya tura Shettima UN
A wani labarin, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya bai wa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima umarnin wakiltarsa tare da jagorantar tawagar Najeriya zuwa taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81 da za a gudanar a New York, Amurka.
Hakan ya kawo ƙarshen ce-ce-ku-ce kan ko Tinubu zai halarci taron da kansa, bayan jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce a watan Yuli shugaban zai halarci taron.
Tinubu ya bar Abuja zuwa Turai a ranar 30 ga Agusta domin hutun mako uku, inda ya fara da London kafin ya wuce Faransa, lamarin da ya ƙara haifar da tsammanin ba zai halarci taron UNGA ba.
Asali: Legit.ng