Jami'in NDLEA Ya Nutse yayin Farautar Mai Laifi a cikin Kogi

Jami'in NDLEA Ya Nutse yayin Farautar Mai Laifi a cikin Kogi

  • Wani jami’in NDLEA ya mutu bayan ya nutse a Kogin Ethiope yayin da yake kokarin kama wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi
  • Lamarin ya faru ne a Obiaruku, karamar hukumar Ukwuani ta Jihar Delta, a karshen makon da ya gabata
  • Wani jami’in da ya shiga kogin shi ma an ceto shi, yayin da wanda ake zargin ya tsere ta cikin kogin ba tare da an cafke shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Delta - Wani jami’in hukumar NDLEA a jihar Delta ya mutu bayan ya nutse a Kogin Ethiope yayin da yake bin wani da ake zargi da aikata laifin da ya shafi miyagun kwayoyi.

An ce lamarin ya faru ne a karshen makon da ya gabata a garin Obiaruku, da ke karamar hukumar Ukwuani ta Jihar Delta.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan mutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Jami'in NDLEA ya rasu a Delta
Taswirar jihar Delta, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wanda ake zargin ya tsere ta cikin kogin

Rahotan Daily Trust ya ce jami’an NDLEA da ke yankin sun kama wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, wanda ake zargin yana safarar haramtattun kwayoyi.

Jami’an sun kai shi kusa da gadar Kogin Ethiope, da alama domin daukarsa zuwa wurin da za a ci gaba da tsare shi.

Sai dai majiyoyi sun ce wanda ake zargin ya kubuta daga hannun jami’an, sannan ya tsalle cikin kogin domin guje wa kamun.

Jami’an NDLEA sun shiga kogin

Wata majiya ta ce jami’an NDLEA sun shiga cikin kogin domin bin wanda ake zargin da kokarin sake kama shi.

Sai dai lamarin ya koma abin takaici, inda daya daga cikin jami’an ya nutse ya rasa ransa yayin aikin.

An kuma ce wani jami’in da ya shiga kogin an ceto shi, sannan aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci.

Wanda ake zargin da jami’an ke bi shi ma ya samu damar tserewa ta cikin kogin.

Kara karanta wannan

Matsayar addinin Musulunci kan sayen hannun jarin matatar Dangote

An gano gawar jami’in

Wata majiya da ta tabbatar da faruwar lamarin ta bayyana abin da ya faru a matsayin abin mamaki, tana mai cewa kogin bai yi zurfin da za a yi tsammanin mutum zai nutse ya mutu ba.

Majiyar ta ce daga bisani an gano gawar jami’in, sannan aka mika ta ga NDLEA bayan an gudanar da wasu al’adun gargajiya da ake yi wa mutanen da suka mutu ta hanyar nutsewa a Kogin Ethiope.

NDLEA ta fara bincike

Da aka tuntubi Kwamandan NDLEA na Jihar Delta, Halilu Hamidi, ya mayar da ‘yan jaridar ga kakakin hukumar na kasa, Femi Babafemi, domin samun bayani.

Sai dai wani jami’in NDLEA ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakkun abubuwan da suka faru da kuma tabbatar da ainihin musabbabin mutuwar jami’in.

Ya ce binciken zai taimaka wajen gano yadda lamarin ya faru da kuma abin da ya haddasa nutsewar jami’in a kogin.

Kara karanta wannan

"Ka da ku": Shawarar Sanusi II ga masu son sayen hannun jarin matatar Dangote

Jami'in NDLEA ya mutu a kogi
Jami'an NDLEA a bakin aiki Hoto: NDLEA
Source: Facebook

An kashe jami'in NDLEA a Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jami'in NDLEA da ke jihar Bauchi ya rasa ransa bayan wani mutum da ba a san ko wanene ba ya caka masa wuka.

Rundunar NDLEA ta ayyana wanda ake zargin da aikata kisan a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo, yayin da ake kokarin gano sunansa da adireshinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng