Tinubu ko Atiku? Jam'iyyar APGA Ta Nuna Ɗan Takarar da Za Ta Mara wa baya a 2027

Tinubu ko Atiku? Jam'iyyar APGA Ta Nuna Ɗan Takarar da Za Ta Mara wa baya a 2027

  • APGA ta ce ba ta miƙa sunan ɗan takarar shugaban ƙasa ga INEC ba saboda ta amince da goyon bayan Bola Tinubu a zaɓen 2027
  • Jam'iyyar ta tabbatar da cewa ta miƙa sunayen dukkan 'yan takararta na Majalisar Dokoki ta Tarayya da ta jihohi cikin wa'adin doka
  • APGA ta ce rashin ɗan takarar shugaban ƙasa ba gazawa ba ce, illa matakin siyasa da NEC ta amince da shi bayan doguwar tattaunawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jam'iyyar APGA ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta miƙa sunan ɗan takarar shugaban ƙasa ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) domin zaɓen 2027 ba.

APGA ta bayana cewa hakan ya biyo bayan matsayar jam'iyyar na mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya sake neman wa'adi na biyu.

Kara karanta wannan

2027: Jam'iyyu 3 sun makara har INEC ta rufe karbar sunayen 'yan takara

Jam'iyyar APGA ta ce za ta goyi bayan Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Gwmanan Anambra, Charles Chukwuma Soludo, a wajen yakin neman zaben jam'iyyar APGA gabanin zaben gwamnan jihar na 2025. Hoto: @CCSoludo
Source: Facebook

INEC za ta goyi bayan Tinubu a 2026

Kakakin jam'iyyar na ƙasa, Mazi Ejimofor Opara, ya shaida wa Vanguard cewa Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na APGA ya yanke wannan hukunci ne bayan tattaunawa mai zurfi.

Mazi Opara ya ce kwamitin ya amince cewa jam'iyyar ba za ta tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa ba saboda goyon bayan da take bai wa Tinubu.

Opara ya bayyana cewa duk da rashin ɗan takarar shugaban ƙasa, APGA ta cika duk wasu sharuddan zaɓe ta hanyar miƙa sunayen dukkan 'yan takararta na Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da kuma Majalisun Dokokin Jihohi ga INEC cikin wa'adin da aka tanada.

Ya ce bai kamata a dauki rashin sunan ɗan takarar shugaban ƙasa a shafin INEC a matsayin gazawa wajen bin ƙa'idojin zaɓe ba, domin mataki ne da jam'iyyar ta ɗauka bisa tsarin siyasa.

Jam'iyyar ta mayar da hankali kan majalisu

Kakakin APGA ya jaddada cewa goyon bayan da jam'iyyar ke bai wa Tinubu a matakin shugaban ƙasa ba zai hana ta fafatawa a zaɓen 'yan majalisu ba.

Kara karanta wannan

A karshe, INEC ta yi matsaya kan takarar Atiku da 'yan ADC a 2027

Ya ce jam'iyyar na da burin ƙarfafa tasirinta a Majalisar Tarayya da Majalisun Dokokin Jihohi ta hanyar tabbatar da nasarar 'yan takararta a zaɓen 2027, in ji rahoton Punch.

APGA ta ce Tinubu za ta goya wa baya a zaben 2027
Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @CCSoludo
Source: Twitter

An buƙaci magoya baya su haɗa kai

Opara ya buƙaci mambobi da magoya bayan APGA su ci gaba da haɗa kai wajen mara wa 'yan takarar jam'iyyar baya a zaɓen majalisu, tare da ci gaba da goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Ya ce bayanin ya zama dole ne saboda yadda jama'a suka fara tambayar dalilin da ya sa babu sunan ɗan takarar shugaban ƙasa na APGA a shafin miƙa sunayen 'yan takara na INEC, bayan jam'iyyar ta ayyana goyon bayanta ga Tinubu.

APGA ta amince Tinubu ya yi tazarce

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamnan Anambra ya ce APGA ta amince da Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takararta a zaben shugaban kasa na 2027.

Gwmamna Charles Soludo ya tunatar da Tinubu cewa APGA ta goyi bayan shugaban ƙasa mai ci a 2011, don haka za ta goyi bayansa a 2027.

Mai girma gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da Tinubu ya je Anambra domin ƙaddamar da ayyukan da aka kammala a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com