Mahara Sun Kutsa Sun Tashi Bam a Masallaci, Mutane da Dama Sun Mutu
- Aƙalla mutane 16, ciki har da jami’an ’yan sanda biyar, sun mutu bayan wata mota ɗauke da bama-bamai ta kutsa cikin wani masallaci Arewa maso Yammacin Pakistan
- Ana ci gaba da musayar wuta tsakanin maharan da jami’an tsaro a masallacin da ke kusa da hedikwatar ’yan sanda a gundumar Kohat
- Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa an kashe ɗaya daga cikin maharan, yayin da ake ci gaba da aikin ceto
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Pakistan — Aƙalla mutane 16, ciki har da jami’an ’yan sanda biyar, sun mutu bayan wata mota ɗauke da bama-bsmsi ta kutsa cikin wani masallaci a Pakistan.
Rahotanni sun nuna cewa an kai wannan mummunan harin bam din ne a wani masallaci da ke Arewa maso Yammacin Pakistan, a cewar wani babban jami’in ’yan sanda a yankin Peshawar.

Source: Getty Images
BBC News ta ruwaito cewa na ci gaba da musayar wuta tsakanin maharan da jami’an tsaro a masallacin da ke kusa da hedikwatar ’yan sanda a gundumar Kohat ta lardin Khyber Pakhtunkhwa.
Wani jami’in yankin ya ce an kashe ɗaya daga cikin maharan, yayin da ake ci gaba da aikin ceton mutane a masallacin.
An kira harin da kunar bakin wake
A cikin wata sanarwa da aka fitar, shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari ya bayyana jimaminss kan wannam hari, tare da fatan samun sauƙin gaggawa ga waɗanda suka jikkata sakamakon fashewar.
Babban Sufeto-Janar na ’yan sandan Khyber Pakhtunkhwa, Zulfikar Hameed, ya bayyana harin a mats8ayin “harin kunar bakin wake”, a cewar rahoton tashar Al-jazeera.
Ya zuwa yanzu, babu wata ƙungiya da ta fito ta ɗauki alhakin kai harin yayin fa Firaministan Pakistan, Muhammad Shehbaz Sharif, shi ma ya yi Allah-wadai da harin bam din.
An samu ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga
A cikin ’yan watannin nan, an samu ƙaruwa sosai a ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a yankunan kan iyakar Pakistan, inda suka fi kai hari kan sojoji da ’yan sanda.
Gwamnatin kasar Pakistan ta ce ’yan bindigar na amfani da mafaka a Afghanistan wajen horaswa da kuma shirya hare-hare a Pakistan.
Sai dai gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta musanta zargin, tana mai cewa matsalar ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai matsala ce ta cikin gida ta Pakistan.
An kai hari masallaci a kasar Amurka
A wani labarin na daban, kun ji cewa mutane uku sun mutu bayan wani harin bindiga da aka kai masallacin cibiyar addinin Musulunci ta San Diego da ke California a kasar Amurka.
Jami’an tsaro sun ce ana binciken harin a matsayin 'harin kiyayya ga Musulmai', yayin da wadanda ake zargi, wasu mutum biyu suka bakunci lahira a wurin.
Shugaban ‘yan sandan San Diego, Scott Wahl, ya bayyana lamarin amatsayin abin tashin hankali ga kowace al’umma, yana mai cewa mahaifiyar daya daga cikin wadanda ake zargi ta kira ‘yan sanda sa’o’i biyu kafin harin.
Asali: Legit.ng

